Labaran garkuwa da mutane
Yan bindiga sun kai farmaki yankin ƙaramar hukumar Giwa a jihar Kaduna, sun yi awon gaba da dagacin Tunburku, Malam Ashiru da wasu manoma a karshen mako.
Amina Adamu, daya daga cikin matan auren da aka sace su a hanyar Takum-Katsina-Ala a jihar Taraba makonni hudu da suka gabata, ta tsero daga hannun masu garkuwa.
Rundunar ƴan sanda reshen jihar Katsina ta bayyana cewa jami'anta sun samu nasarar kama mutum buyu da ake zargi da hannu a sace mahaifiyar Dauda Rarara.
Rahotanni sun nuna cewa ƴan bindiga kusan 100 sun shiga kauyen Dambaza a ƙaramar hukumar Maradun ta jihar Zamfara, sun yi garkuwa da mutane akalla 47.
'Yan bindiga sun kai farmaki garin Kahutu da ke ƙaramar hukumar Ɗanja a jihar Katsina, sun yi awon gaba da mahaifiyar fitaccen mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara.
Yan bindigan da suka yi garkuwa da limamin coci, Mikah Suleiman sun ɗauki bidiyonsa yana neman agajin mutane, ya ce rayuwarsa na cikin haɗari a wurin ƴan fashi.
Rundunar ƴan sanda ta tabbatar da cewa ta samu rahoton sace wata mata mai tsohon ciki yayin da take hanyar zuwa asibiti a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.
Dakarun rundunar sojojin Najeriya sun yi nasarar ƙara rage mugayen iri a sassa daban-daban na ƙasar nan cikin mako 1, sun ceto ɗaruruwan mutanen da aka sace.
Masu garkuwa da mutane ɗauke da manyan bindigu sun tafi da Madakin Shabu jim kaɗan bayan ya fito daga Masallaci lokacin Sallar Isha'i a jihar Nasarawa.
Labaran garkuwa da mutane
Samu kari