Labaran garkuwa da mutane
Masu garkuwa da mutane ɗauke da manyan bindigu sun tafi da Madakin Shabu jim kaɗan bayan ya fito daga Masallaci lokacin Sallar Isha'i a jihar Nasarawa.
Sojojin Najeriya sun samu nasarar cafke wasu mutane biyu da ake zargi da garkuwa da mutane a garuruwan jihar Taraba. Wadanda ake zargin sun ba da bayanai.
Kasurgumin dan ta'adda, Bello Turji ya ce kafa shari'a da Ahmed Sani Yarima ya yi a Zamfara ce ta jawo aka fara cin mutuncin Fulani wanda hakan ya jawo ta'addanci.
Wasu miyagun 'yan bindiga sun hallaka wani matashi bayan ya kai musu kudaden fansa a jihar Kaduna. 'Yan bindigan sun ce ya yi musu tsaurin ido ne.
Wau ‘yan bindiga da ake zargin mazauna Binuwai ne sun dira yankin Gugur da ke karamar hukumar Katsina-Ala tare da kashe mutane shida a harin ramuwar gayya.
Wasu 'yan bindiga da ake ganin masu garkuwa da mutane ne sun yi savuwar aika-aika a jihar Legas. 'Yan bindigan sun sace manajan darakta na kamfani.
Gwamnan Zamfara ya ce sai a kama ‘yan bindiga, amma alkali ya ba da belinsu a kotu. Dauda Lawal Dare ya tabbatar da cewa matsalar rashin tsaro ya fi karfinsa.
Wata kungiya mai zaman kanta ta bukaci shugaban kasa Bola Tinubu ya sanya wa'adi ga shugabannin tsaro kan magance matsalar tsaro a Najeriya baki daya.
Wasu yan bindiga su hudu sun kai hari kan jami'an yan sanda a safiyar yau talata inda suka kashe yan sanda biyu da farar hula daya. Mutanen yankin suna zaman dar dar
Labaran garkuwa da mutane
Samu kari