Katsina
Sauki ya fara samuwa a wasu jihohi Arewa maso yamma, yayin da farashin abinci ya fara yin kasa a wasu daga cikin kasuwannin yankin ciki har da Kano da Katsina.
Gwamnan jihar Katsina, Mallam Dikko Umaru Radda, ya tafi ziyarar aiki zuwa kasar China. Gwamnan ya tafi ziyarar ne bayan ya dawo hutun kwanaki 30.
Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindiga sun kai hari gidan wani hadimin gwamnan Katsina inda suka kashe shi da uwar gidansa tare da kuma sace amaryarsa.
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta yi nasarar kamata wata mata mai shekara 30 dauke da bindiga za ta kaiwa wani hatsabibin dan fashi da ya addabi jihar Katsina.
Gwamnatin jihar Katsina ta janye dokar hana fita gaɓa ɗaya da ta sanya a faɗin kananan hukumomin jihar sakamakon abubuwan da suka faru a lokacin zanga zanga.
Gwamnatin jihar Katsina ta yabawa Shugaba Bola Tinubu kan nadin 'yan jihar Katsina mukamai daban-daban wanda ake ganin na daga cikin salon sakawa Muhammadu Buhari.
Gwamnatin jihar Katsina ta sake sassauta dokar hana fita da ta sanya a fadin jihar. Gwamnatin ta dauki matakin ne biyo bayan ingantar da halin tsaro ya yi a jihar.
Gwamnatin jihar Katsina ta mika sakon godiya ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bayan raba manyan mukamai ga yan jihar da suka hada da Aminu Bello Masari.
Mukaddashin gwamnan jihar Katsina, Malam Faruk Lawal Jobe, ya bayar da izinin sassauta dokar hana zirga-zirga ta sa’o’i 24 a karamar hukumar Dutsinma.
Katsina
Samu kari