Allah Ya yiwa marubucin littafin 'Kulba na barna', Umaru Kasagi, rasuwa

Allah Ya yiwa marubucin littafin 'Kulba na barna', Umaru Kasagi, rasuwa

Allah Ya yi wa shahrarren marubucin Hausa kuma dan wasan kwaikwayo, Umaru Danjuma Katsina rasuwa.

Danjuma wanda aka fi sani da Kasagi na Halima ya rasu ne da safiyar ranar Juma’a 29 ga watan Oktoba, 2021, rahoton Aminiya.

Kasagi ne ya rubuta shararren littafin da ake karantawa daliban sakandare 'Kulba Na Barna'.

Rahoton ya kara da cewa marigayin dan kwaikwayon ya rasu ne a wani asibiti a Katsina, bayan gajeruwar jinya.

An haife shi ne a jihar Katsina a shekarar 1950 kuma ya yi karatu a Najeriya da Ingila, inda ya kware a fannin fina-finai, riwayar BBC.

Ya bar mata biyu da 'ya'ya 13.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Read also

Da Dumi: An tsinci gawar ƴan bindiga 3 da suka kashe kansu wurin faɗan rabon kuɗin fansa a wata jihar Arewa

Umaru Kasagi, ya rasu
Allah Ya yiwa marubucin littafin 'Kulba na barna', Umaru Kasagi, rasuwa Hoto: Magazine
Source: UGC

Source: Legit.ng

Online view pixel