An kuma kai hari: Miyagun yan bindiga sun hallaka mutum 6, sun sace wasu dama a jihar Katsina

An kuma kai hari: Miyagun yan bindiga sun hallaka mutum 6, sun sace wasu dama a jihar Katsina

  • Yan bindiga sun sake kai sabon hari a jihar Katsina, sun kashe aƙalla mutum shida tare da sace wasu adadi mai yawa na mutane
  • Rahoto ya nuna cewa maharan sun farmaki ƙauyen Unguwar Samanja a Faskari ana gab da sallar Magrib
  • Wani mazaunin Daudawa ya koka kan yadda yan bindiga ke cigaba da aikin ta'addancinsu a Faskari duk da matakan da gwamnati ta ɗauka

Katsina - Rahotanni sun bayyana cewa miyagun yan bindiga sun kashe aƙalla mutum 6, sun yi awon gaba da wasu a wani sabon hari da suka kai jihar Katsina.

Jaridar Premium Times tace maharan sun kai harin ne ƙauyen Unguwar Samanja dake ƙaramar hukumar Faskari a jihar Katsina.

Jihar Katsina dai, itace jihar da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya fito kuma tana fama da hare-haren yan bindiga.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga: Sarkin Birnin Gwari ya bayyana alherin da katse hanyoyin sadarwa ya jawo

Sabon hari a Katsina
An kuma kai hari: Miyagun yan bindiga sun hallaka mutum 6, sun sace wasu dama a jihar Katsina Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Yadda lamarin ya faru

Mazauna Daudawa dake makwaftaka da ƙauyen, sun shaidawa manema labarai cewa yan bindigan sun shiga ƙauyen da misalin ƙarfe 5:49 na yamma, lokacin da mutane ke shirin sallan Magrib.

Ƙaramar hukumar Faskari, na ɗaya daga cikin yankunan dake fama da yawaitar hare-haren yan bindiga a jihar Katsina.

Kuma Faskari tana ɗaya daga cikin ƙananan hukumomi 13 da gwamnati ta ɗauki matakin datse hanyoyin sadarwa domin magance matsalar.

Wata ƙungiyar al'umma dake garin Daudawa, ta koka cewa duk da matakan da gwamnatin jiha ta ɗauka, har yanzun yan bindiga na cigaba da ta'addanci a Faskari.

Harin ya yi muni sosai

Wani mazaunin Daudawa, Nasir Hassan, yace maharan sun shiga ƙauyen ne akan mashina mintuna kaɗan kafin Magrib, inda suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi.

Kara karanta wannan

Sabon hari: 'Yan bindiga sun kai hari masallaci, sun bindige masallata a jihar Neja

Yace:

"Daga labarin da na samu, mutum 5 sun mutu, kuma an gudanar da jana'izarsu ranar Litinin da safe."
"Sun kuma ƙone gidaje da shagunan mutane kafin su fita kauyen, an faɗa mun ba su saci komai ba, sun dai ƙona shaguna."

Hassan wanda ɗalibin makarantar gaba da sakandire ne a Zamfara, yace maharan sun yi awon gaba da mutane amma bai san adadin su ba.

A wani labarin kuma Yan bindiga sun kutsa kai wurin Ibada ana tsaka da bauta, Sun yi awon gaba da mutum 3

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun yi awon gaba da masu bauta mutum uku kuma sun nemi miliyoyin kuɗin fansa.

Rundunar yan sandan jihar tace jami'anta sun bazama neman maharan tare da ceto mutanen da aka sace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel