Kasashen Duniya
A labarin nan, za a ji cewa Pakistan tana aiki ba dare ba rana domin a samu damar kawo sulhu mai dorewa a tsakanin Iran da kasar Amurka a cikin ruwan sanyi.
Ministan tsaron Pakistan, Khawaja Asif ya bayyana cewa Isra'ila ce babbar matsala a duniyar yau, ta zama karfen kafa ga al'ummar duniya wajen zubar da jini.
Shugabannin Rasha da Ukraine sun amince da tsagaita wuta na sa'o'i 32 bayan shafe shekaru suna yakar juna. Vladimir Putin ya ce an yi haka ne saboda Easter.
Tsohon ministan harkokin wajen Iran, Dr Kamal Kharrazi ya rasu bayan wani harin da Amurka da Isra'ila suka kai gidan shi bayan kashe matar shi a kwanakin baya.
An sake bude masallacin Kudus ga masu ibada a Isra'ila bayan kwanaki 40 da Isra’ila ta rufe shi, inda dubban Falasdinawa suka hallara sallar asuba.
Yakin Amurka/Isra'ila da Iran d aya shafe kwana 40 kafin tsagaita wuta ya jawo faruwar abubuwa da dama. Mun tattaro muku abubuwa 10 da suka faru a yakin da aka yi.
Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya umurci fara tattaunawar zaman lafiya da Lebanon cikin gaggawa, ciki har da batun kwance damarar kungiyar Hezbollah.
Shugaban Faransa, Emmanuel MAcron ya yi Allah wadai da harin Isra'ila a Lebanon bayan tsagaita wuta da aka yi. Yai yi magana da Amurka da kasar Iran.
Gwamnatin kasar Rasha ta yi magana kan tsagaita wuta da aka yi tsakanin Iran da Amurka. Ta bayyana Hormuz a matsayin makamin nukiliyar kasar Iran.
Kasashen Duniya
Samu kari