Ahmad Lawan
Barau Ibrahim Jibrin ya shiga sahun wadanda za su nemi shugabancin Majalisar Dattawa. Da yiwuwar Sanatan Arewacin Kano ya gwabza da Orji Uzor Kalu a takarar.
‘Yan Majalisa da yawa sun rasa Kujerunsu a 2023. Shugaban majalisar wakilan tarayyan Femi Gbajabiamila ya zargi masu zabe da amfani da addini da kabilanci.
'Yan Majalisa 7 Daga Jihohin Arewa su na neman kujerar shugabancin majalisar wakilan tarayya ganin cewa zai yi wahala Femi Gbajabiamila ya zarce a karo na biyu.
Mun kawo cikakken jerin ‘Yan siyasan da INEC ta ba takardar shaidar lashe zaben Majalisa. Mata 2 rak su ka shiga jerin ‘Yan siyasa 109 da za su zama Sanatoci.
Alhassan Ado Doguwa yana sha’awar zama Shugaban majalisa, sannan Sani Musa, Barau Jibrin, Orji Uzor Kalu, Godswill Akpabio su na harin kujerar Ahmad Lawan.
Har mun fahimci wadanda suka sake lashe zaben Majalisa sun fara yi wa sababbin Sanatoci kamfe. Godswill Akpabio da Uzor Kalu su na neman kujerar Shugaban Kasa
Za a samu jerin Sanatoci da Za a tantsar a Majalisar daga Abuja da Jihohi 36. Babu cikakken sakamakon Enugu, Imo, Taraba, Yobe, Borno, Kebbi, Zamfara, da Filato
Nan da kusan watanni uku ake sa ran za a rantsar da sabuwar majalisar tarayya. Za a samu sababbin Sanatoci da ‘Yan majalisar da suka doke wadanda suka dade.
Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmed Lawan ya ce mutanen mazabarsa sun masa yankar dabobi da azumi saboda ya yi nasarar zarcewa kan kujerarsa a zaben 2023
Ahmad Lawan
Samu kari