Mataimakin Shugaban APC Ya Cire Musulmai a Cikin 'Yan Takarar Shugabancin Majalisa

Mataimakin Shugaban APC Ya Cire Musulmai a Cikin 'Yan Takarar Shugabancin Majalisa

  • Mataimakin Shugaban APC na Arewa bai yarda Musulmi ya zama Shugaban Majalisa a bana ba
  • Salihu Lukman yana da ra’ayin cewa Kirista ya fi cancanta ya karbi shugabancin majalisar dattawa
  • Ganin Bola Tinubu da Kashim Shettima Musulmai ne, Lukman yana ganin za a murkushe Kiristoci

Abuja - Mataimakin shugaban APC na shiyyar Arewa maso yamma, Salihu Lukman ya ce bai dace Musulmi ya nemi shugabancin majalisar dattawa ba.

A ranar Litinin, The Cable ta rahoto shugaban jama’iyyar mai-mulki yana cewa duk mai harin wannan kujera, bai ganin darajar kundin tsarin mulki.

Salihu Lukman ya yi wannan magana ne ganin cewa zababben shugaban kasa, Bola Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima duka Musulmai ne.

Lukman ya ce yunkurin tsaida wani Musulmi ya zama shugaba a majalisar tarayya, zai jawo addinin Musulunci ya yi baba-kere a gwamnatin kasar.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: Yadda dan kasar waje ya shigo Najeriya da kayan hodar iblis a cikin kwaroron roba

Ba a nemi zaman lafiya ba - Lukman

A ra’ayin daya daga cikin manyan ‘yan majalisar NWC a jam’iyyar APC, hakan ba zai kawo zaman lafiya ba yayin da ake neman kwanciyar hankali.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Majalisa
Shugabancin Majalisa Hoto: @NgrSenate
Asali: Facebook
"Duk Musulmin da ya ke neman mukamin shugaban majalisar dattawa, bai ganin darajar tsarin mulkin Najeriya da na jam’iyyar APC.
Dalili kuwa shi ne sashe na 14(3) na kundin tsarin mulki ya fito karara ya ce dole a tafi da kowane bangare wajen kafa gwamnatin tarayya.
Wajibi a rika damawa da kowane bangare wajen aikin, kuma akwau bukatar a kawo zaman lafiya ta hanyar hana wani bangare baba-kere.
Tun da aka samu Musulmai biyu da za a rantsar a matsayin shugaban kasa da mataimaki a ranar 29 ga watan Mayu, yunkurin samun Musulmin shugaban majalisar dattawa zai jawo Musulmai su yi rinjaye a gwamnatin tarayya, kuma wannan zai taba zaman lafiya da kwanciyar hankalin Najeriya a matsayin kasa, wanda ba za a yarda da wannan ba.

Kara karanta wannan

Takarar Majalisa ta Dauki Zafi, Ana Sauraron Dawowar Tinubu Bayan Kwana 18 a Kasar Waje

- Salihu Lukman

Cin hanci domin samun mukami

Tribune ta rahoto Lukman yana cewa abin kunya ne wasu masu neman kujerar su na kauce hanya.

‘Dan siyasar yana magana kan zargin wasu Sanatoci da bada cin hanci domin samun mukamin, a cewarsa duka biyu daga Arewa maso yamma suke.

Sauyi a NNPP, LP da PDP

Abba Kawu-Ali zai jagoranci NNPP mai alamar kayan dadi, kafin nan an ji labari cewa shi ne shugaban jam'iyya na sashen Arewa maso gabas.

Yadda PDP ta kori Dr. Iyorchia Ayu, LP ta rasa Julius Abure, Jam’iyyar NNPP ta yi sabon shugaba bayan Farfesa Rufai Ahmed Alkali yayi murabus.

Asali: Legit.ng

Online view pixel