Fulani Makiyaya
Jakadan Amurka a Najeriya, Richard Mills ya gana da kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah domin jin matsalolin makiyaya a yankunan Najeriya da samar da mafita.
Kungiyar makiyaya ta sanar da cewa an kai hari kan shanu da wani makiyayi a karamar hukumar Riyom ta jihar Filato inda aka kashe shanu 37 da bindiga.
Ana fargabar cewa Fulani makiyaya sun kai hari a garin Gbagir, jihar Benue da safiyar Juma’a, sun kashe Kiristoci 10, sun jikkata 25, yayin da gwamnati ta yi martani
Fusatattun matasa sun kai farmaki garuruwan Fulani a Kaiama, jihar Kwara, bisa zargin suna taimaka wa 'yan bindiga; an kama masu garkuwa da mutane tara a Ekiti.
Gwamnatin Filato ta fara bincike kan saka guba wa shanun wani makiyayi a karamar hukumar Bassa. An kafa kwatin bincike domin tabbatar da gaskiyar lamarin.
Hare-haren da aka kai kan garuruwa biyar a Bokkos sun yi sanadiyyar mutuwar mutum goma. BCDC ta yi kira ga jama’a su kare kansu daga barazanar ‘yan ta’adda.
Rundunar 'yan sanda a jihar Zamfara ta kama mutum 15 bayan Fulani makiyaya sun gwabza fada mai muni da Hausawa. An samu gawar wani matashi cikin jini.
'Yan sanda sun musanta jita-jitar da ake yadawa kan kai wa Inyamurai Igbo hari a Kano, sun fara bincike don kama wadanda ke yada karyar, tare da yin babban gargadi.
Rahotanni sun tabbatar da cewa ‘yan bindiga sun kashe shugaban Miyetti Allah a Filato bayan buda baki. An taba kai masa hari sau uku kafin daga karshe a kashe shi.
Fulani Makiyaya
Samu kari