Tsadar Mai
Ministan yada labarai Najeriya, Mohammed Idris ya kare matakin cire tallafin mai da Shugaba Bola Tinubu ya yi a watan Mayun shekarar 2023 a Abuja.
Ministan yada labarai, Mohammed Idris Malagi ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su kara hakuri akan sauye-sauyen gwamnatin Bola Tinubu, ya jaddada cewa akwai alkairi.
Ministan wutar lantarki a Najeriya, Adebayo Adelabu ya bukaci cire tallafin wutar kantarki don samar da ita yadda ya kamata ganin yadda basuka suka yi yawa.
Gwamnan jihar Imo kuma shugaban gwamnonin APC ya shawarci 'yan Najeriya kan yi wa Shugaba Tinubu adalci a cikin watanni takwas kacal da ya yi a gwamnati.
Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya amince da biyan naira dubu 35 ga ma'aikatan jihar don rage musu radadi bayan cire tallafin mai a Najeriya baki daya.
Ya zuwa yanzu dai manyan kamfanoni bakwai ne suka yi rijistar fara dillancin man Dangote, kuma sun kammala duk wata yarjejeniya da matatar, aiki kawai za su fara.
Bayan dakatar da shirin NSIPA da sauran abubuwan da ke karkashin shirin, Tinubu ya kafa kwamitin bincike don gano bakin zaren a yau Asabar 13 ga watan Janairu.
Ana tsaka da tsadar man fetur a Najeriya, Shugaba Tinubu ya tura wa shugaban NNPC sako a ranar Litinin. Tinubu ya taya Mele Kyari murnar cika shekaru 59.
Kungiyar kare hakkin dan Adam da wayar da kan jama'a, CHRICED ta bayyana cewa Shugaba Tinubu ya biye wa Bankin Duniya wurin kara farashin mai da wutar lantarki.
Tsadar Mai
Samu kari