Babban kotun tarayya
NDLEA ta gurfanar da Sulaiman Danwawu a kotun tarayya Kano kan zarge-zarge 8 da suka shafi safarar Tramadol, Rohypnol da Pregabalin ba bisa ka’ida ba.
Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya ce mafi yawan alkalai sun zama masu karɓar na goro, sun daina yi wa jama'a adalci a shari'sr Najeriya.
Kotun Ebonyi ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga mutum hudu da suka hada baki suka kashe Chinonso Elom, wani matashi dan Ngbo, a ranar 5 ga Fabrairu, 2023.
Wata kotu a jihar Ondo ta gurfanar da wani basarake kan zargin cin zarafin mutanensa. Sarkin ya yi wa wasu mutane bulala kan gaza biyan harajin da ya daura musu.
Kotun daukaka kara da ke Abuja ta tanadi hukunci kan shari'o'in da ke neman tsige gwamnan Edo. PDP na kalubalantar nasarar APC, inda ta ce akwai kuskure a zaben.
Bayan watsa takardun Naira da cin mutunci, kotun tarayya da ke Kaduna ta yanke wa Muhammad Kabir hukuncin dauri saboda cin zarafin Naira a wani bidiyo da ya wallafa.
Wata babbar kotu ta yanke wa 'yan TikTok biyu hukuncin daurin watanni shida a Legas saboda wulakanta Naira. EFCC ce ta gurfanar da su bayan samun bidiyo.
Babbar kotun tarayya mai zama a Kano ta sanya ranar 20 ga watan Mayu, 2025 a matsayin ranar da za ta yi hukunci a shari'ar fitacciyar ƴar TikTok, Murja Kunya.
Bayan kotu ta kama Farfesa Peter Oghan da laifin murde zabe, har yanzu yana yawo a gari ba tare da zaman kurkukun shekaru uku da aka yanke masa ba.
Babban kotun tarayya
Samu kari