Jam’iyyar PDP Ta Garzaya Kotun Koli Don Kalubalantar Shari'ar Gwamnan APC, Ta Koka da Zaluncin Kotu

Jam’iyyar PDP Ta Garzaya Kotun Koli Don Kalubalantar Shari'ar Gwamnan APC, Ta Koka da Zaluncin Kotu

  • Bayan yanke hukuncin kotun daukaka kara, jam'iyyar PDP za ta daukaka zuwa kotun koli don neman hakkinta
  • Jam'iyyar na kalubalantar hukuncin kotun daukaka kara da ta yi kan zaben Gwamna Sanwo-Olu na jihar Legas
  • Wannan na zuwa ne bayan kotun ta tabbatar da nasarar Gwamna Sanwo-Olu a matsayin wanda ya lashe zaben

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Legas - Jam'iyyar adawa ta PDP a jihar Legas ta garzaya kotun koli don kalubalantar nasarar Gwamna Sanwo-Olu.

Jam'iyyar ta ce an yi kuskure wurin tabbatar da nasarar Sanwo-Olu a matsayin gwamnan jihar, cewar TheCable

PDP a jihar Legas ta daukaka kara zuwa kotun koli
Jandor na PDP ya daukaka kara zuwa kotun koli. Hoto: Babajide Sanwo-Olu, Abdul'azeez Adediran.
Asali: Facebook

Mene PDP ke cewa kan hukuncin?

Sakataren yada labarai na jam'iyyar a jihar Legas, Hakeem Amode shi ya bayyana haka yayin ganawa da manema labarai.

Kara karanta wannan

APC ta mamaye Majalisar jihar PDP bayan kotu ta kwace dukkan kujeru 16, an shiga yanayi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakeem yayin ganawar a yau Litinin 27 ga watan Nuwamba ya ce kotun daukaka kara ta yi rashin adalci a hukuncin.

A watan Maris, Hukumar INEC ta ayyana Gwamna Sanwo-Olu a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna jihar, Pulse ta tattaro.

Sanwo-Olu ya samu kuri'u 762,134 yayin da dan takarar LP, Gbadebo Rhodes-Vivour ya samu kuri'u 312,329.

Yayin hirar, Amode ya ce sun daukaka kara zuwa kotun koli a kwanakin nan inda ya ce su na fatan samun adalci a can.

Martanin PDP kan shari'ar zaben Legas

Ya ce:

"Mu na kalubalantar hukuncin kotun daukaka kara kuma za mu daukaka kara a 'yan kwanakin nan zuwa kotun koli.
"Ganin yadda wasu hukunce-hukuncen kotun daukaka kara ta kasance, akwai matsaloli da dama a cikin hukuncin.
"A matsayin jam'iyya, mun tabbatar cewa ba a yi hukuncin adalci ba a karar da mu ke yi na zaben watan Maris."

Kara karanta wannan

Bayan Uba Sani, Kotun ɗaukaka kara ta yanke hukunci kan nasarar wani gwamnan APC

Amode ya kara da cewa su na da tabbacin samun hukuncin adalci da kuma gyara kura-kuran baya.

Kotu ta yi hukunci a shari'ar Legas

A wani labarin, kotun daukaka kara ta raba gardama a shari'ar zaben gwamnan jihar Legas.

Kotun ta tabbatar da nasarar Gwamna Sanwo-Olu na jihar Legas a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.