Nade-naden gwamnati
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada Abba Abubakar Aliyu a matsayin shugaban hukumar wutar lantarki ta karkara (REA.) Abba yana rike da REA tun daga Maris din 2024.
Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya fadi matsayarsa ko da kuwa yana cikin gwamnatin Bola Tinubu yayin martani kan zargin sukar APC saboda bai cikin gwamnati.
Malam Nasir El-Rufai ya ba hadimin Bola Tinubu, Daniel Bwala shawara kan rike muƙaminsa inda ya ce tun farko bai son muƙami a gwamnatin Bola Tinubu.
Gwamna Caleb Mutfwang na Plateau ya sallami kwamishinoni biyar daga majalisar zartarwa, inda aka nada sababbi domin maye gurbinsu ba tare da bata lokaci ba.
Gwamnan Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya naɗa sababbin masu ba shi shawara ta musamman, za a ba su rantsuwar kama aiki yau Talata, 28 ga Janairu, 2025.
Gwamnatin Kano ta bayyana cewa an yi sababbin nade-nade domin bayar da damar inganta gudanar da rayuwar mazauna jihar, sannan an nada sabon Akanta Janar.
Shugaban Bola Tinubu ya sanar da nadin shugabannin manyan hukumomi a ranar Juma’a, 24 ga watan Janairu. Legit.ng ta yi karin haske kan 'yan siyasar Kano da aka nada.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya nada shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje da tsohon mataimakinsa, Nasiru Yusuf Gawuna sababbin mukamai.
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya sake gwangwaje tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano, Dr. Nasir Yusuf Gawuna da sabon muƙami a gwamnatin tarayya.
Nade-naden gwamnati
Samu kari