Yan bindiga
Bishop Matthew Hassan Kukah ya ce Najeriya ba za ta kawo ƙarshen ta’addanci da karfin bindiga kaɗai ba, yana mai jaddada bukatar amfani da sulhu da adalci.
Jami'an tsaro sun samu nasarar hallaka wani tantirin dan ta'adda a jihar Kwara. Dan ta'addan ya kware wajen yin garkuwa da mutane don neman kudin fansa.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Zamfara, DSP Yazid Abubakar, ya tabbatar da sace kansiloli biyu a jihar da kuma wani limami bayan idar da sallar mangariba.
Yayin da an bindiga suka addabi jihar Kwara a Arewacin Najeriya, gwamnatin ta tabbatar da mutuwar daya daga cikin jagororin masu garkuwa da mutane, Maidawa.
Wasu miyagun 'yan bindiga sun yi awon gaba da wata malamar asibiti bayan ta yi rantsuwar kama aiki. 'Yan bindigan sun bukaci a ba su kudin fansa masu tarin yawa.
Sojojin Operation Whirl Stroke a jihar Benue sun yi nasara kan wani kasurgumin dan ta'adda inda suka hallaka shi sai dai harsashe ya kashe daliba.
Bayan yada rade-radi kan tsaro a jihar Kwara, Gwamnati ta karyata jita-jitar da ake yadawa cewa hukumar DSS ta kwace makaman yan sa-kai kafin aka kai musu hari.
Jami'an rundunar 'yan sandan jihar Zamfara sun samu nasarar cafke wani hatsabibin dan bindiga. 'Yan sandan sun kuma kwato makamai masu tarin yawa.
Rundunar 'yan sandan jihar Benue ta kama mutum daya bisa zargin harbe wani dan bindigan da ya tuba. Wasu mutane biyu ne suka harbe shi suna tafiya a babur.
Yan bindiga
Samu kari