Miyagun Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Wurin Ibada, Sun Halaka Bayin Allah Da Dama a Ebonyi

Miyagun Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Wurin Ibada, Sun Halaka Bayin Allah Da Dama a Ebonyi

  • Wasu miyagun sun kai hari cocin katolika a babban birnin jihar Ebonyi, sun kashe masu ibada uku ana gobe kirsimeti
  • Limamin cocin, Rabaran Peter Nworie, ne ya tabbatar da haka yayin da yake jawabi a wurin bikin kirsimeti ranar Litinin
  • Ya buƙaci kiristoci su dage da yi wa ƙasar nan addu'ar samun ci gaba da haɗin kai mai ɗorewa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ebonyi - ‘Yan bindiga a jajibirin Kirsimeti sun kai hari wata cocin Katolika da ke Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi, inda suka kashe wasu masu ibada uku.

Bishop na Abakaliki Diocese, Rabaran Peter Nworie ya tabbatar da harin ga manema labarai, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kirsimeti: Yan Shi'a sun halarci bikin a coci, sun fadi kwararan dalilai masu kama hankali

Yan bindiga sun halaka mutane uku a coci a Ebonyi.
Yan bindiga sun kai hari cocin katolika, sun halaka masu ibada a Ebonyi Hoto: Francis Nwifuru
Asali: Twitter

Nworie ya bayyana hakan ne a bikin Kirsimeti na ranar Litinin a Cocin Saint Theresa Cathedral.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce ƴan bindigan sun aikata kisan ne a cocin Immaculate Conception Catholic Church, Nkweagu, da ke karamar hukumar Abakaliki ta jihar Ebonyi.

Lamarin ya auku ne da misalin karfe 11:30 na daren Lahadi, 24 ga watan Disamba, 2023 ana gobe bikin kirsimeti.

Limamin cocin, wanda ya bayyana lamarin a matsayin abin bakin ciki da takaici, ya yi addu’ar Allah ya jikan waɗanda suka rasa rayukansu.

Yadda harin ya faru ranar Lahadi

Ya bayyana cewa maharan sun mamaye cocin ne a lokacin da wani limamin cocin ke gudanar da addu'a, suka kashe wasu tare da jikkata wasu da dama.

A cewar Nworie, irin wannan abin takaici bai taba faruwa a cocin jihar da ke Kudu maso Gabashin Najeriya ba.

Kara karanta wannan

Halin kunci: Ubangiji ba zai yafe maka ba, Fitaccen malamin addini ya taba Tinubu kan salon mulkinsa

Ya ce: “Wannan shi ne karo na farko da irin wannan abu ya faru a coci da kuma jihar Ebonyi baki daya."

Tun a farko, malamin cocin ya yi wa'azin jan hankali ga al'umma da su yi amfani da koyarwar kirsimeti a harkokin su na yau da kullum.

Ya roƙi ɗaukacin mabiya addinin kirista su roƙi Allah haɗin kai da ci gaba ga jihar Ebonyi da ƙasar nan baki ɗaya.

Harin yan bindiga na Filato ya ƙara munana

A wani rahoton kuma Adadin mutanen da suka mutu a hare-haren da ƴan bindiga suka kai kananan hukumomi 2 a Filato ya haura 100.

Ciyaman ɗin riƙon karamar hukumar Bokkos, Monday Kassah, ya ce zuwa yanzu sun gano gawarwaki 113 tare da masu rauni 300.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel