Sojoji Sun Ceto Mutane 52 a Hannun 'Yan Bindiga Yayin Wani Artabu, an Bayyana Matakin Gaba

Sojoji Sun Ceto Mutane 52 a Hannun 'Yan Bindiga Yayin Wani Artabu, an Bayyana Matakin Gaba

  • Sojojin Najeriya sun kwato akalla mutane 52 wadanda 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar Sokoto
  • Rundunar ta Hadarin Daji a jiya Juma'a 22 ga watan Disamba ta yi nasarar ceto mutanen ne a karamar hukumar Isa da ke jihar
  • Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a shafin X a yau Asabar 23 ga watan Disamba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Sokoto - Rundunar sojin Najeriya ta yi nasarar kwato wandanda aka yi garkuwa da su 52 a jihar Sokoto.

Rundunar ta Hadarin Daji a jiya Juma'a 22 ga watan Disamba ta yi nasarar ceto mutanen ne a karamar hukumar Isa da ke jihar.

Kara karanta wannan

Jimami yayin da mahaifiyar tsohon Kakakin Majalisar Wakilai ta rasu ta na da shekaru 103

Rundunar sojin Najeriya sun ceto mutane 52 daga hannun 'yan bindiga
Sojoji kwato mutane 52 daga hannun 'yan bindiga a Sokoto. Hoto: Nigeran Army.
Asali: Facebook

Yaushe aka ceto mutanen?

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a shafin X a yau Asabar 23 ga watan Disamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce an yi nasarar kubutar da wadanda aka sacen ne a ranar Juma'a 22 ga watan Disamba a wasu dazukan kauyuka uku.

Dazukan sun hada da na Kubuta da Saruwa da Gundumi a karamar hukumar Isa a jihar, cewar Daily Post.

Wace sanarwa rundunar ta fitar?

Sanarwar ta ce:

"A samu nasarar ce a ranar 22 ga watan Disamba bayan rundunar sun kai farmaki dazukan kauyuka guda uku.
"Dauzukan sun hada da na Saruwa da Kubuta da kuma Gundumi a karamar hukumar Isa a jihar.
"Yayin farmakin, rundunar ta yi nasarar ceto wadanda aka yi garkuwa da su guda 52 yayin da 'yan ta'adda da dama suka hallaka."

Kara karanta wannan

INEC ta saka ranar sake zabe don cike gurbin kujerun da kotu ta rushe da sauransu, ta tura gargadi

Daga cikin wadanda aka kubutar din sun hada da maza 14 da mata 32 da kuma yara kanana guda shida, cewar Punch.

Rundunar ta kara da cewa za a kai su don binciken lafiyarsu da kuma mika su ga iyalansu bayan kammala duk abin da ya kamata.

Mutane 3 sun tsere daga hannun 'yan bindiga

A wani labarin, akalla mutane 3 suka tsere daga sansanin 'yan bindiga a jihar Kaduna a makon da ya gabata.

Mutanen na daga cikin mutane 11 da maharan su ka sace a wani mummunan hari da suka kai a jihar.

Tuni aka kai wadanda abin ya shafa asibiti don kula da lafiyarsu tare da mika su ga iyalansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel