Yan bindiga
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa ya damu matukan kan matsalar rashin tsaro a Arewacin Najeriya. Ya ce gwamnatinsa na daukar matakai.
Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), ta musanta rahotannin da ke cewa 'yan bindiga sun nemi kudaden fansa kan dalivan da suka yi garkuwa da su a jihar Neja.
Makarantar St Mary Papiri da ke jihar Neja ta fitar da bayani cewa adadin daliban da aka sace a harin 'yan bindiga ya kai 303 bayan an nemi dalibai 88 an rasa.
Sanannen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi, ya yi magana kan yawaitar hare-haren sace dalibai a wasu jihohin Najeriya.
Majalisar dinkin duniya ta yi Allah wadai kan sace daliban da 'yan bindiga suka yi a jihar Neja. Ta bukaci a gaggauta kokarin tabbatar da cewa an kubutar da su.
Gwamnatin jihar Kebbi karkaahin jagorancin, Gwamna Nasir Idris, ta yi zargin cewa an janye dakarun sojoji kafin 'yan bindiga su sace dalibai zuwa daji.
‘Yan sanda a Kwara sun karyata bidiyon kama wadanda suka kai hari a cocin Eruku, sun ce labarin karya ne kuma ana ci gaba da aikin ceto wadanda aka yi garkuwa da su.
Kungiyar Kiristoci ta Najeriya reshen Neja ta bayyana cewa mutane 227 ciki har da malamai da dalibai ne yan bindiga suka yi garkuwa da su a makarantar Katolika.
Ministan tsaro Bello Matawalle ya isa Birnin Kebbi domin aiwatar da umarnin Shugaba Tinubu na hanzarta ceto dalibai akalla 25 na GGCSS Maga da aka sace.
Yan bindiga
Samu kari