Yan bindiga
Rahotanni sun tabbatar da cewa wani fitaccen ɗan bindiga a jihar Katsina, Abu Radde da yaransa sun miƙa wuya ga jami’an tsaro inda suka saki mutum goma.
'Yan bindigan da suka yi garkuwa da tsohon shugaban hukumar kula da masu yi wa kasa hidima (NYSC), Birgediya Janar Maharazu Tsiga, na ci gaba da tsare shi.
‘Yan bindiga sun kashe manoma 9 a yankin Karaga, inda suka sace mutane 6 a Farin-Doki, tare da kwashe shanu. Halin tsaro a Neja na kara tabarbarewa.
Rundunar tsaron Najeriya ta kashe 'yan ta'adda 217, ta kama 574 tare da ceto mutane 320 a watan Fabrairu. 'Yan ta'adda 152 ne suka mika wuya ga sojojin Najeriya.
'Yan bindiga dauke da makamai sun yi aika-aika a jihohin Zamfara da Katsina. 'Yan bindigan sun salwantar da rayukan mutum biyar tare da sace wasu zuwa cikin daji.
Rundunar 'yan sanda ta kama wasu 'yan bindiga masu garkuwa da mutane su 20. 'Yan sanda sun kai farmaki ne maboyar 'yan ta'addar a kusa da wata gona.
Wasu tsagerun 'yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun hallaka jami'an 'yan sanda. 'Yan sandan sun rasu ne yayin wani artabu da suka yi.
Kungiyar ci gaban zaman lafiyabta matasa a Arewa maso Yamma, NWYPD ta yabawa salon jagorancin hafsan tsaro, Janar Christopher Musa a yaki da ta'addanci.
Dakarun sojojin Najeriya masu aikin samar da tsaro sun samu nasarar dakile wani harin 'yan bindiga a jihar Katsina. Sojojin sun fatattaki 'yan bindigan.
Yan bindiga
Samu kari