Yan bindiga
Wasu miyagun 'yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a babban birnin tarayya Abuja. 'Yan bindigan sun yi awon gaba da wata soja da wasu mutum biyu.
Jami'an tsaro sun karyata kai hari jami'ar Maiduguri inda suka bayyana cewa harbe-harben da aka ji sun faru ne a Ajilari da ke jihar Borno a Arewacin Najeriya.
Wasu miyagu sun farmaki masallaci a jihar Kaduna yayin da masallata suke tsaka da gudanar da ibada. 'Yan sanda sun cafke wasu da ake zargi da kai harin.
Gwamnatin Benue ta tabbatar da mutuwar sojoji biyu, inda mataimakin gwamna Sam Ode ya ce sun rasu ne yayin kare fararen hula daga harin 'yan bindiga a yankin Kwande.
Rahotanni sun tabbatar da cewa ‘yan bindiga sun kashe shugaban Miyetti Allah a Filato bayan buda baki. An taba kai masa hari sau uku kafin daga karshe a kashe shi.
‘Yan bindiga sun sace dalibai 2 a jami’ar FUDMA, da ke jihar Katsina yayin da aka ceto wani wanda aka yi garkuwa da shi a Adamawa, an kuma kama malami a Jigawa.
Wasu fusatattun masu zanga-zanga sun nuna bacin ransu kan kisan da 'yan bindiga suka yi wa manoma a jihar Ondo. Sun mamaye gidan gwamnatin jihar.
‘Yan sanda sun kama masu safarar makamai, miyagun kwayoyi da jabun kuɗi a samame daban-daban, inda suka cafke masu hannu a laifuka tare da kayayyakin haram.
Gobara ta kama tashar bututun mai a River bayan abubuwan fashewa sun fashe a wani hari da aka kai jihar yayin da ake tsaka da maganar tsige gwamna Fubara.
Yan bindiga
Samu kari