Kaduna: Sojin Sun Halaka ‘Yan Bindiga 9, Sun Ceto Mata da Kananan Yara

Kaduna: Sojin Sun Halaka ‘Yan Bindiga 9, Sun Ceto Mata da Kananan Yara

  • Zakakuran dakarun sojin runduna ta musamman na sojin kasan Najeriya sun halaka ‘yan bindiga tara a yankunan karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna
  • An halaka biyar daga cikin miyagun bayan dirar mikiya da sojojin suka yi a sansaninsu dake Rafin Sarki, yayin da aka sheke hudu a dajin Galadima
  • Sojojin sun yi nasarar ceton jama’a masu tarin yawa da suka hada da mata da kananan yara da miyagun suka yi garkuwa dasu a sansanoninsu

Kaduna - Dakarun sojin Najeriya dake karkashin runduna ta musamman ta Sojin kasa sun halaka ‘yan bindiga 9 har maboyarsu dake karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna.

Taswirar jihar Kaduna
Kaduna: Sojin Sun Halaka ‘Yan Bindiga 9, Sun Ceto Mata da Kananan Yara. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

Kamar yadda kwamishinan tsaron cikin gida na jihar, Samuel Aruwan ya bayyana, dakarun sun halaka ‘yan bindiga biyar a Rafin Sarki sai wasu hudu a dajin Galadimawa duk a karamar hukumar Giwa.

Aruwan a takardar da ya fitar ga manema labarai a ranar Alhamis a shafinsa na Twitter, bai bayyana ranar da aka yi wannan aikin ba.

Duk da haka ya bayyana cewa gomman mata da kananan yara aka ceto yayin aikin kuma an samo bindigogin toka biyar, harsasai hudu, rediyo da caja, kayan sojoji da sauransu daga maboyar ‘yan ta’addan.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kwamishinan yace:

“Dakarun rundunar soji ta musamman karkashin sojojin kasa sun kai farmaki tare da halaka ‘yan bindiga tara yayin wata musayar wuta mai tsanani a wasu sassan karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna.
“A bayanin da aka kawo wa gwamnatin jihar Kaduna, an bayyana cewa dakarun sun kakkabe sansanin ‘yan bindiga dake wuraren Rafin Sarki kuma suna halaka biyar yayin da sauran suka arce.
“A wani artabu na daban, dakarun sun kakkabe maboyar miyagun dake wurin dajin Galadimawa inda suka halaka ‘yan bindiga hudu. Gomman mutane ne da aka yi garkuwa dasu da suka hada da mata da kananan yara ne aka ceto bayan wadanda suka sace su sun arce.”

Aruwan ya cigaba da cewa:

“A yayin sake duba inda lamarin ya faru, dakarun da ke shirye kan ko ta kwana sun samo bindigogin toka biyar, harsasai, rediyo da caja, kayan sojoji da sauransu.
“Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya yabawa dagewar sojojin kuma yana mika godiya garesu kan nasarar da suke samu tare da ceto jama’a.
“Ana cigaba da duba duk maboyar ‘yan ta’adda a fadin jihar.
“Gwamnatin jihar Kaduna tana rokon jama’a da su taimaka da bayanai kan ‘yan bindiga, maboyarsu tare da masu kai musu bayanai da kayayyaki ta wadannan Lambobin wayoyin: 09034000060; 08170189999.”

Yan Sanda Sun kama miyagu 7, sun ceto mutum 15

A wani labari na daban, rundunar ‘yan sandan jihar a Zamfara ta tabbatar da damke ‘yan bindiga 7 da ransu a maboyarsu.

Bayan musayar wutan da aka yi, ‘yan sandan sun ceto wasu mutum 15 da miyagun suka yi garkuwa dasu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel