Yan Bindiga Sun Yayan Shahararren Jarumin Fina-Finan Najeriya

Yan Bindiga Sun Yayan Shahararren Jarumin Fina-Finan Najeriya

  • Hankula sun tashi a Owerri, babban birnin jihar Imo, lokacin da yan bindiga masu dabakka dokar zama a gida suka kai hari, suka kashe dan sanda da yayan jarumin Nollywood, Osita Iheme
  • Abin bakin cikin ya faru ne a birnin Owerri da kuma hanyar Orlu-Owerri a karamar hukumar Mbaitoli da ke jihar Imo
  • Yayin da Iheme ya rasu nan take, kwamishinan ma'adinan kasa yana can a asibiti saboda harbi da sara da aka masa

Imo - Yan bindiga sun kai wa mutanen garin Mbaitoli a jihar Imo hari da rana a yau Juma'a domin tabbaka dokar zama-a-gida na kwana 5, The Punch ta rahoto.

Yan bindigan sun kai hare-hare a wurare daban-daban, inda suka kashe dan sanda da Prince Iheme, yayin jarumin fina-finai, Osita Iheme da aka fi sani da Pawpaw.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun farmaki na gaban goshin Atiku a jihar gwamnan PDP mai adawa da Atiku

Pawpaw
Yan Bindiga Sun Yayan Shararren Jarumin Fina-Finan Najeriya. Hoto: The Nation
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yan bindigan kuma sun sari kwamishinan albarkatun kasa, Martin Eke, rahoton The Nation.

An tattaro cewa yan bindigan sun taho a mota kirar Tundra suka rika bude wuta hakan yasa mutane suka tarwatse.

Mutane sun rufe shagunansu, titi ya yi wayam a yayin da masu motocci suka fice suka bar motoccinsu.

A Orji, kusa da Owerri, yan bindigan sanye da bakaken kaya a motocci uku sun kai wa mutane hari, har da dan sanda.

Wani shaidan gani da ido ya shaidawa wakilin The Nation cewa yan bindigan sun tarar da dan sandan a 7up Junction a Orji kuma suka bindige shi har lahira.

Ya ce:

"Yanzu suka kashe dan sanda. Sun bude musu wuta kuma suna ihun cewa akwai dokar zama a gida. Mun fada muku ku tafi gida. Kada ku fito."

Kara karanta wannan

Alhamdulillahi: Fitaccen sarkin da 'yan bindiga suka sace a wata jiha ya shaki iskar 'yanci

Wani shaidan da ya ce ya sha da kyar ya ce:

"Na tsallake rijiya da baya yanzu. Sun tsayarda mu kuma suka yi harbi a iska suka ce mu tafi gida. Ba su harbe mu ba saboda ina cikin wasu dattawan mata."

An kuma tattaro cewa yan bindigan da ke sunyi harbe-harebe tserewa a kasuwar Nkwo-Orji kafin suka tafi Okigwe Road.

Yadda aka halaka Iheme

A Ubomri a karamar hukumar Mbaitoli, yan bindigan sun tare tawagar yan takarar majalisa na APC na yankin Mbaitoli/Ikeduru, Amaradi Amadi.

Yayin da aka bindige Prince Iheme aka kashe shi nan take, an sari Eke da adda.

Wata majiya ta jadada cewa:

"Prince Iheme yana cikin mota daya tare da kwamishinan albarkatun kasa, Martin Eke. Prince Iheme, wanda yayan Pawpaw ne an kashe shi nan take. Kwamishinan da aka rantsar sati biyu da suka wuce kuma ya jikkata. An garzaya da shi asibiti. Sun tafiya a mota kirar Ford. Ina fatan ya murmure."

Kara karanta wannan

Da zafi-zafi: 'Yan sanda sun ceto wasu mutum uku da aka sace jiya da dare a Abuja

Martanin IPOB

Kakakin IPOB, Emma Powerful ya yi kira ga mutane kada su raga wa duk wanda ke jadda dokar zama a gida dole.

Ya ce:

"Mun fada musu su sheke dun wanda ke kokarin jadada dokar zama a gida ko su kira lambar da aka basu don jami'an ESN su iso wurin."

Kakakin yan sandan Imo, Micheal Abattam, bai riga ya amsa sakon tambaya kan lamarin da aka masa ba.

Yan bindiga sun sace malaman addini 2 a Jihar Plateau

Wasu miyagun yan bindiga da ba a san ko su wanenen ba sun sace malamai biyu a Mararrabar Jema'a da ke karamar hukumar Jos ta Kudu.

Hakan ya faru ne a yayin da malaman ke hanyar Mangu zuwa Jos kwatsam maharan suka tare su suka tisa keyarsu misalin karfe 8 na daren Laraba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel