Matsin tattalin arziki
An tafka ta'asa yayin gudanar da zanga-zanga ta ranar farko a birnin Kano da kewaye inda jama'ar gari da 'yan daba su ka rika satar kayan jama'a.
Rahotanni sun bayyana cewa an kashe wasu matasa guda hudu da ke aiki a wani gidan mai a jihar Borno yayin da zanga-zangar yunwa ta rikide zuwa tashin hankali.
Wasu fusatattun matasa sun kona hedikwatar jam'iyyar APC yayin da suka wawushe kayan da ke ciki. An ce masu zanga-zangar sun kuma lalata kadarorin jihar Jigawa.
Gwamnatin Kaduna ta ce babu wata dokar hana fita da aka sanya a jihar. Uba Sani ya ce yanzu an dawo da kwanciyar hankali a jihar bayan ta'addancin masu zanga-zanga.
Matasan Najeriya masu zanga zanga a dandalin Eagle Square sun dakile ministan matasa, Ayodele Olawande daga yin magana yayin da suke zanga zanga a Abuja.
Ana cigaba da zanga-zanga a fadin Najeriya baki daya inda a halin yanzu ya rikide ya koma tashin hankali a manyan biranen Arewacin kasar a yau Alhamis.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana takaicin yadda marasa kishin jihar su ka shiga cikin masu gudanar da zanga-zanga wajen tayar da hankula da sata a jihar.
Gwamnatin jihar Yobe ta sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 a yankunan Potiskum, Gashua da Nguru na jihar bayan da wasu ‘yan daba suka kwace zanga-zanga.
Rahotannin da muke samu sun tabbatar da cewa masu zanga-zanga a birnin Abuja sun durfafi yankin Asokoro inda ke dauke da manyan kasar Najeriya a yau Alhamis.
Matsin tattalin arziki
Samu kari