Matsin tattalin arziki
Ibrahim Ayuba Isa, wanda ya ke dan jarida ne a Kano da ke daukar rahoto kan zanga zanga ga gidan talabijin din TVC ya shaidawa Legit cewa da kyar ya tsira.
Magoya bayan shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a jihar Kano sun gudanar da zanga-zangar adawa da masu kin manufofin gwamnatin tarayya, inda su ka ce a kara lokaci.
Rahotanni sun bayyana cewa daruruwan masu zanga-zanga sun haddasa cunkoson ababen hawa a hanyar Abuja zuwa Kaduna bayan toshe titi a Suleja da ke jihar Neja.
Jami'an ƴan sanda sun tarwatsa masu zanga-zangar da suka matsa sai sun ga mai martaba sarkin Bauchi, sun harba masu barkonon tsohuwa mai sa hawaye.
Kungiyar lauyoyi ta kasa, NBA za ta ba masu zanga zanga da aka zalunta kariya kyauta a dukkan jihohin Najeriya. NBA ta yi umurni da saka ido a fadin Najeriya.
Yayin da aka fara gudanar da zanga-zanga a jihohin kasar nan 36 da babban birnin tarayya Abuja, an shiga fargabar za a iya samun matsalar tsaro a kasa.
Yayin da ake sa ran fara zanga-zangar gama gari a fadin Najeriya daga yau Alhamis 1-10 Agusta, 2024, wani lauya, Ebun Olu Adegboruwa ya nemi a rage kwanakin fita.
Gwamnatin Tarayya ta bayyana dalilin kin sanar da wuraren siyar da shinkafa mai nauyin 50kg kan kudi N40,000 kacal inda ta ce ta yi hakan ne domin dalilai na tsaro.
Gwamnonin jihohi sun ja kunnen masu zanga zanga su bi hankali ban da yin duk wani abu da zai iya kawo tashin tashin a tsawon lokacin da za su ɗauka.
Matsin tattalin arziki
Samu kari