Dan takara
Dan takarar kujerar shugabancin kasar nan a inuwar Labour Party yace yana ganin girman manyansa don haka ko me za ayi, ba zai iya taba Alhaji Atiku Abubakar ba
Rahoton nan ya tattaro abin da aka ji daga bakin Atiku, Kwankwaso da Peter Obi a wajen muhawara. Gidan talabijin Arise TV suka shirya taron domin jin ta bakinsu
‘Dan takaran Peoples Democratic Party, Atiku Abubakar yace Gwamnonin da ke mulki sun nemi su hana a rika aikawa kananan hukumomi kudinsu tsakanin 1999 da 2007.
Maganar da ake yi. Peter Obi mai neman mulki a LP, ya samu goyon bayan wasu manya a Najeriya, kuma an ji LP tana da jama’n da za su taimaka mata a zaben 2023.
Wasu Shugabanni na reshen jihar Ogun sun kori Doyin Okupe wanda babban jigo ne daga Jam’iyyar LP, hakan yana nufin an samu baraka a takarar Peter Obi a 2023.
Sadiq Ango Abdullahi ya fada hannun 'yan bindiga a watan Maris yayin da aka shirya zaben tsaida gwani na neman takarar majalisa a Mayu, sai ga shi ya samu tuta.
Za a ji ‘Dan takaran shugaban kasa ya bata lokaci wajen kawo takardun shiga kotu. Ganin dan takarar ya bata lokaci, lauyansa da na jam’iyya za su biya N20000.
Babachir David Lawal yace ba a maganar APC a wadanda za su iya cin zabe. Festus Keyamo yace abin ban dariya ne a fadin haka duba da karfin da suka yi a siyasa.
Ana so a wargaza gaba daya kwamitin neman takarar Peter Obi bayan ganin cewa 'da takara da kujerun Shugabannin jam'iyya na kasa duk su na hannun 'Yan Kudu.
Dan takara
Samu kari