Tsofaffin Shugabannin Najeriya 2 Sun Zama ‘Yan Obidient, Suna Goyon Bayan Peter Obi

Tsofaffin Shugabannin Najeriya 2 Sun Zama ‘Yan Obidient, Suna Goyon Bayan Peter Obi

  • Farfesa Pat Utomi yace an samu tsofaffin Shugabannin Najeriya da ke goyon bayan Peter Obi
  • Utomi ya halarci zaman da BIG TENT ta shirya, ya yi wa ‘Yan tafiyar Obidients wannan albishir
  • A cewar Farfesan, jam’iyyar LP tana da mutanen da za ta lashe zaben Najeriya da za ayi a 2023

Abuja - Pat Utomi wanda Farfesan siyasar tattalin arziki ne a Najeriya, yayi wa magoya bayan Peter Obi albishir a game da zaben shugaban kasa.

A wata zantawa da ya yi da jama’a a garin Abuja, Punch ta rahoto Farfesa Pat Utomi yana cewa tsofaffin shugabannin kasa biyu suna tare da Peter Obi.

BIG-TENT, wata gamayyar kungiyoyi, jam’iyyun siyasa da tafiyar masu zaman kansu ta shirya wannan zama da aka yi da jagoran na jam’iyyar LP a jiya.

Kara karanta wannan

Jami'iyar APC Nakasu Kawai Ta Kawo A Nigeria Tsawon Lokacin da ta Shafe Tana Mulki, Atiku

Pat Utomi ya fito yana cewa manyan jam’iyyun siyasan da ake tunkaho da su a kasar nan watau APC mai mulki da kuma PDP ba su kafu a kasa irin LP ba.

Utomi: Mu ke da mutane a kasa

A cewarsa, jam’iyyar LP ce take da jama’an da za su taimaka mata wajen lashe zabe, ta karbe shugabanci daga hannun masu mulkin da suka kashe kasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dukiya kurum ba su isa su sa a ci zabe ba, Farfesan ya yi watsi da tasirin kudi a siyasa.

Tsofaffin Shugabannin Najeriya
Peter Obi a gonar Olusegun Obasanjo Hoto: www.nairaland.com
Asali: UGC
"Kudi kurum ba su sa a ci zabe. Tsofaffin shugabannin Najeriya biyu sun fada mani sun shigo cikin Obidients.
Mutane da-dama suna son bin tafiyar ba tare da shigowa LP ba, domin ganin Obi da Baba-Ahmed sun yi nasara, a karbe kasar nan daga wadanda suka rike kasa.

Kara karanta wannan

Ya’yan Buhari sun shiga yakin neman zaben mata na Tinubu-Shetima a Katsina

Jam’iyyar LP ta fi PDP da APC kafuwa, idan ana maganar jama’a, kusan sai in yi dariya, domin ba su fahimci ma’anar jama’a ba.
Maganar da suke yi ta gungun mutane marasa gaskiya ne da suka iya murde zabe, dole mu daina wannan, ba wannan ne jama’a ba."

Su wanene ke goyon bayan Peter Obi?

Kamar yadda The Cable ta kawo rahoto a yammacin Asabar, Utomi bai iya bayyana wadannan tsofaffin masu mulki da ke goyon bayan ‘dan takaransu ba.

Kwanakin baya aka ji labari Mahadi Shehu ya ce makasudin zuwa Olusegun Obasanjo Arewa shi ne tallata takarar Peter Obi ga dattawan da ke yankin.

Mai kamfanin Dialogue Group ya ce Obasanjo yana tare da Obi a zaben 2023, yana kokarin ganin ‘dan takaran na LP ne ya yi galaba a takarar shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel