An Ci Tarar ‘Dan Takarar Shugaban Kasa Saboda Makara Wajen Gabatar da Takardu

An Ci Tarar ‘Dan Takarar Shugaban Kasa Saboda Makara Wajen Gabatar da Takardu

  • Ana shari’a tsakanin Kola Abiola mai neman Shugaban kasa a People’s Redemption Party da Patience Key
  • A zaman kotun da aka yi, Alkali tace Lauyoyin jam’iyyar PRP da na Abiola su biya tarar kudi ga Lauyan Madam Key
  • Ana fama da wannan shari’a ne a lokacin da Kola Abiola yake kamfe domin zama shugaban Najeriya a inuwar PRP

Abuja - Babban kotun tarayya mai zama a garin Abuja ta ci tarar Kola Abiola mai neman zama shugaban kasar Najeriya a karkahsin jam’iyyar PRP.

An samu Kola Abiola da laifin gaza gabatar da takardun kotunsa a lokacin da ya kamata. Daily Trust ta fitar da rahoton nan a ranar Asabar dinnan.

Alkali Fadima Aminu wanda ta saurari karar, ta ci tara a kan ‘dan takaran shugaban kasar.

A ranar 25 ga watan Nuwamba 2022, kotu ta saurari karar da Patience Ndidi Key ta shigar a game da zaben tsaida ‘dan takaran shugaban kasa na PRP.

An saurari karar Patience Ndidi Key

Hakan na zuwa ne bayan Patience Ndidi Key wanda ta nemi tikitin shugaban kasa a PRP ta shigar da karar jam’iyyar, hukumar INEC da Latifu Abiola.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

NAN tace bayan sauraron karar Madam Patience Ndidi Key, kotu ta bukaci kowane bangare ya shigar da takardunsa kafin ranar da za a sake zama.

Kola Abiola
Shugaban Kasa tare da Kola Abiola Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Abin da ‘yar siyasar take so shi ne a ruguza zaben da ya ba Abiola nasarar zama ‘dan takara,

Jaridar nan ta Vanguard tace Madam Key ta bukaci Alkali ta tunbuke Abiola a matsayin ‘dan takarar shugaban kasa a zaben da za ayi a 2023.

Lauyoyi sun ki biyan kudin kara

Lauyar PRP, Regina Audu da kuma Lauyan ‘dan takaran, Ijeoma Madu sun koka da cewa sun gagara biyan kudin kara saboda matsalar rashin sabis.

Da aka koma kotun, Magnus Ihejirika wanda shi ne Lauyan mai shigar da kara, ya zargi Lauyoyin masu bada kariya da batawa kotu lokacinta da gan-gan.

Mai shari’a Fadima Aminu tayi watsi da bukatun lauyoyin wadanda ake kara, ta bukaci jam’iyyar PRP da Abiola duk su biya N20, 000 ga Ijeoma Madu.

Sai nan da 2 ga watan Disamban 2022 kotun tarayyar za ta cigaba da sauraron wannan shari’a. Rahoton nan ya zo a jaridar Aminiya a ranar Asabar.

Tinubu ya yi raddi ga tsohon SGF

A hasashen da ya yi, an ji labari dazu cewa Injiniya Babachir David Lawal yace ba a maganar Jam’iyyar APC a wadanda za su iya cin zaben shekarar badi.

Keyamo yana tunkaho da Gwamnonin Jihohi, ‘Yan majalisar tarayya da kwararren ‘dan takara baya ga rikicin da ya dabaibaye PDP a cikin dalilan nasara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel