
ASUU







Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ta dage kaddamar da shirin ba daliban Najeriya lamuni mara ruwa don karatunsu.

NLC ta ce an yi mata barazana iri-iri domin a yi watsi da gama-garin zanga-zangar da ta gudanar. Kwamred Joe Ajaero ya ce kungiyar NLC ba za ta ja da baya ba.

Kungiyar malaman jami’o’i ta shiyyar Akure, ta yi Allah-wadai da rashin tallafin da ake ba wa ilimi, ta ce rashin ilimi ne ya jawo yawaitar masu garkuwa da mutane.

Kungiyar malaman jami'o'i ta ƙasa ASUU ta nuna damuwa kan halin matsin da aka shiga a Najeriya sakamakon wasu matakai da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya ɗauka.

Bola Tinubu ya jika hantar ma’aikatan jami’a bayan bakar wahala a zamanin Buhari. Gwamnati tana neman hada fada a jami’o’in kasar a dalilin albashin da aka saki.

Yayin da ake cikin mummunan hali a Najeriya, kungiyar ASUU ta ce ta rasa Farfesoshi 46 saboda tsadar rayuwa a Jami'o'in birnin Abuja da Minna da Keffi.

Gwamnatin tarayya karkashin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ta fara biyan albashin malaman jami'o'i na kungiyar ASUU da aka rike saboda yajin aikin da suka yi.

Kungiyar ASUU ta na barazanar shiga yajin-aikin farko a mulkin Bola Tinubu. Farfesa Emmanuel Osodeke ya nuna cewa ana neman hana su hakkokinsu sai sun daina aiki.

Tsohon ministan ilmi, Farfesa Tunde Adeniran, ya bayyana cewa yan Najeriya na rububin zuwa Jamhuriyar Benin samo digirin bogi saboda cin hancin dake kasar nan.
ASUU
Samu kari