Jami’ar Ibadan Ta Kara Kudin Makaranta da 480%, Karatun Gwamnati Ya Kara Tsada

Jami’ar Ibadan Ta Kara Kudin Makaranta da 480%, Karatun Gwamnati Ya Kara Tsada

  • Jami'ar Ibadan ta dauki haramar kara kudin makaranta ga sababbin ɗalibai a zangon karatu na shakarar 2024
  • Karin kudin zai kai kashi 480 cikin 100 inda kudin zai kai sama da dubu ɗari huɗu maimakon dubu saba'in zuwa tamanin a baya
  • Duk da cewa hukumar makarantar ba ta yi karin bayani a kan ƙarin kudin ba, daliban sun nuna yadda aka kara musu kuɗin makarantar a shafin yanar gizon su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Hukumar gudanarwar jami’ar Ibadan (UI) ta fara duba yiwuwar karin kudin da sabbin dalibai za su biya wanda karin zai kai kashi 480 cikin 100.

An tattaro cewa bayanin karin kudin an buga shi a shafin yanar gizon Jami'ar.

Kara karanta wannan

Bikin Sallah: 'Yan sanda a Kano sun kama mutum 54 masu yunkurin hargitsa hawan sallah

University of Ibadan
Sabbin dalibai zasu biya sama da N40, 000 a jami'ar Ibadan Hoto: Uiniversity of Ibadan
Asali: Facebook

Da farko an ruwaito shugaban al’amuran dalibai na jami'ar, Keye Abiona, yana tabbatar da karin kudaden, amma daga baya ya ki yin karin bayani kan lamarin lokacin da jaridar Leadership ta tuntubesa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayanin kakakin jami'ar Ibadan

Kakakin jami’ar, Adejoke Akinpelu, ya ce, nan bada jimawa ba cikakken bayanin yadda farashin kudin makarantar na shekarar 2024 zai kasance zai bayyana a shafin yanar gizon makarantar.

“An keɓance kuɗaɗen ne ga ɗaliban bisa la’akari da kwasa-kwasan karatunsu kuma za a sanya su a shafin yanar gizon jami'ar daga gobe ko kuma daga baya," a cewarsa

Daga bakin wanda abin ya shafa

Ɗaliban da abun ya shafa sun yi bayani akan karin kudin tare da nuna yadda aka kara musu kuɗin.

Daya daga cikin daliban ya nuna cewa N412,000 ne kudin da aka sanya zai biya a zangon karatun shekarar 2024, cewar jaridar The Cable

Kara karanta wannan

Wuraren shakatawa 5 da ya kamata ku ziyarta yayin bukukuwan Sallah a Kaduna

Wani daga cikinsu kuma ya nuna N203,500 a matsayin jimillar kudaden jami’a da sabon dalibi zai biya a shekarar 2024.

Sauran dalibai a wasu tsangayun kuma sun bayyana cewa ba su sami damar shiga shafin yanar gizonsu ba balle su ga jimillar kudin da zasu biya.

Wani dalibi da ya shiga jami’ar a shekarar 2023 ya tabbatar da cewa a baya an biya kudin da bai wuce N64,600 zuwa N69,600 ba.

Karin da aka samu ya kai kashi 492.5 cikin 100, duk da cewa karin ya banbanta lura da kwas din da dalibi zai karanta.

Jami'o'i mafi inganci a duniya

A wani rahoton, kun ji cewa jerin ingantattun jami'o'i da Times Higher Education ta yi ta sanya jami'ar Ibadan a matsayin na 801 cikin 978 na mafi ingantattun jami'o'i a fadin duniya.

Jami'ar Ibadan kadai ce jami'ar Najeriya da ta samu shiga cikin jeri.

Asali: Legit.ng

Online view pixel