ASUU Ta Bayyana Dalili Daya da Ke Ta’azzara Garkuwa da Mutane a Najeriya

ASUU Ta Bayyana Dalili Daya da Ke Ta’azzara Garkuwa da Mutane a Najeriya

  • Ƙungiyar malaman jami'o'i (ASUU) ta ce rashin muhimmancin da gwamnati ke ba jami'o'i ne ya jawo yawaitar masu garkuwa da mutane
  • Kodinetan kungiyar na shiyyar Akure, Dr. Adeola Egbedokun ya ce abun Allah-wadai ne yadda jami'o'i ke rasa kuɗaɗen tallafin karatu
  • Egbedokun ya kuma zargi gwamnati da ƙin cika alkawarin da ta daukarwa ASUU na yin watsi da tsarin IPPIS wajen biyan malaman jami'a albashi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Osun - Kungiyar malaman jami’o’i ta shiyyar Akure, da ta hada da jihohin Osun, Ondo, da Ekiti, sun yi Allah-wadai da rashin tallafin da ake ba wa fannin ilimi.

Dr Adeola Egbedokun, kodinetan kungiyar ASUU na shiyyar Akure ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a jami’ar Obafemi Awolowo, Ile-Ife, jihar Osun.

Kara karanta wannan

"A shigo da abinci" TUC ta gano hanya 1 da zata share hawayen talakawa, ta aike da saƙo ga Tinubu

ASUU ta fadi abin da ya jawo yawaitar garkuwa da mutane
ASUU ta zargi gwamnati da gaza cika alkawarin da ta dauka na daina amfani da IPPIS wajen biyan albashin malamai. Hoto: @asuunews, @PBATMediaCentre
Asali: Twitter

Dokta Egbedokun, ya ce rashin samun tallafin karatu na taimakawa wajen yawaitar munanan laifuka musamman garkuwa da mutane a kasar nan, kamar yadda The Punch ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rashin ilimi ne jefa mutane garkuwa da mutane

Ya kuma zargi gwamnatin tarayya da gaza cika alkawarin da ta dauka na yin watsi da tsarin IPPIS wajen biyan albashin malaman jami’o’i.

Ya ce:

“Gwamnati ba ta da gaskiya game da tallafin ilimi. Ta yaya gwamnati za ta shirya tarurruka da dama tare da sanya hannu kan yarjejeniyoyi amma ta ki aiwatar da wadannan yarjejeniyoyin?
"Yawancin wadannan mutanen da ke haifar da rashin tsaro, masu tayar da kayar baya, watakila saboda ba su samu isasshen ilimi ba ne."

Egbedokun ya yi nuni da cewa rashin samar da tallafin ilimi yadda ya kamata ne ya jawo turjiya daga malaman jami'o'i saboda rashin biyan su albashi.

Kara karanta wannan

An bayyana wadanda suka zuga Tinubu ya tafka babban kuskure kan rikicin Nijar

Har yanzu malaman jami'a na bin bashin albashi

A halin yanzu da muke magana, wasu na can sun fake a cikin daji suna neman wadanda za su yi garkuwa da su domin gwamnati ta dakile su daga samun ilimi, rahoton Nigerian Bulletin.

Da yake kara jawabi, Egbedokun ya ce amfani da IPPIS wajen biyan wani bangare na albashin 'yan kungiyar ASUU ya sabawa yarjejeniyar da aka kulla da kungiyar.

Ya kara da cewa da yawa daga cikin malaman jami'o'i har yanzu na bin bashin albashi na watanni 6 zuwa 36.

An kama ƙasurgumin mai garkuwa da mutane a Abuja

A wani labarin kuma, rundunar ƴan sandan babban birnin tarayya ta kama ƙasurgumin mai garkuwa da mutane, Abu Ibrahim, wanda ya addabi garuruwan Abuja da satar mutane.

Idan ba a manta ba, Abu Ibrahim shi ne cikon mutum na biyu da ministan Abuja, Nyesom Wike ya saka ladar naira miliyan 20 ga duk wanda ya kama su don ayi masu hukunci.

Rundunar ta ce ta kama Abu Ibrahim a wani dajin Sardauna da ke garin Toto, jihar Nasarawa kuma ta fara gudanar da bincike don gurfanar da shi gaban kotu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel