Yajin aikin ASUU
Babu maganar yajin-aikin kungiyar ASUU a jami’o’i Idan Bola Ahmed Tinubu ya na mulki. Tinubu ya je taron yaye daliban jami’ar FUTO, ya dauki alkawarin gyara ilmi.
Shugaban NLC ya zo Jihar Imo ne su na kus-kus da zabe, Gwamna Hope Uzodinma ya ce siyasa ya shigasa, shiyasa aka laka masa dukan shiga yajin-aiki.
Kungiyar kwadago ta NLC, ta lissafa sunayen wasu jami'an gwamnati, 'yan sanda, ciki har da tsohon kwamishan 'yan sanda na jihar Imo da take so a hukunta.
Majalisar dattawan Najeriya ta buƙaci kungiyoyin kwadago na ƙasa su hakura su janye yajin aikin da suka fara domin nuna suna kishin ƙasa da bin doka da oda.
Gwamnatin tarayya ta shiga ganawa da kungiyoyin NLC da TUC don tattauna hanyoyin da za a bi don kawo karshen yajin yajin gama gari da kungiyoyin suka shiga.
Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya yi magana kan yadda wasu bankuna su ke gudanar da ayyukansu a lokacin da ake yajin aiki a faɗin ƙasar nan.
Jami'ar Bayero da ke Kano (BUK) ta sanar da dakatar da gudanar da jarabawar zangon karatun farko na shekarar 2022/2023 saboda yajin aikin ƙungiyoyin ƙwadago.
NLC ta bayar da umurnin tsunduma yajin aikin ne a taron majalisar zartarwa na kungiyoyin kwadago na kasa da aka gudanar a ranar 13 ga watan Nuwamba, 2023 a Abuja.
Harkoki sun daina tafiya a ma'aikatun tarayya da na jiha a babban birnin jihar Delta yayin da NLC ta tsunduma yajin aikin sai baba ta gani daga ranar Talata.
Yajin aikin ASUU
Samu kari