Shugaba Tinubu Ya Bayyana Hanya 1 da Za a Bi Domin Kawo Karshen Yajin Aiki a Najeriya

Shugaba Tinubu Ya Bayyana Hanya 1 da Za a Bi Domin Kawo Karshen Yajin Aiki a Najeriya

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi magana kan hanyar da za a kawo ƙarshen yawaitar yajin aikin malaman jami'o'i
  • Shugaban ƙasar ya yi bayanin cewa tattaunawa da hawa teburin sulhu ita ce kaɗai za ta kawo ƙarshen yajin aiki
  • Shugaba Tinubu ya yi nuni da cewa lokaci ya yi da malaman jami'o'in za su cigaba da bincike domin gogayya da takwarorinsu a duniya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da ƙalubalen da jami’o’in Najeriya ke fuskanta, yana mai cewa gwamnatin tarayya na aiki tuƙuru domin ganin ta magance su, cewar rahoton Daily Trust.

Tinubu, yayin da yake jawabi a wajen taron yaye ɗalibai karo na 24 na Jami’ar Maiduguri da aka gudanar a Maiduguri a ranar Asabar, ya bayyana cewa, hanyar tattaunawa ce kawai za ta yi maganin matsalolin da ake fuskanta da ƙungiyoyin malaman jami'o'i.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya roƙi 'yan Najeriya muhimmin abu 1 da zai taimaka wajen yaƙar ta'addanci a arewa

Shugaba Tinubu ya yi magana kan yajin aiki a Najeriya
Shugaba Tinubu ya ce tattaunawa ce kawai za ta yi maganin yajin aiki a Najeriya Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter
"Gwamnati ba za ta iya yi ita kaɗai ba, a shirye muke mu tattauna, hanya ɗaya tilo da za a magance matsaloli da ƙungiyoyin malaman jami'o'i domin ciyar da ɓangaren ilimi gaba, ita ce ta hanyar tattaunawa." A cewarsa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya yi muhimmin kira ga malaman jami'o'i

Tinubu wanda mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya wakilta, ya ce lokaci ya yi da malaman jami'o'i za su koma bincike domin samun cigaba a fannin kimiyya da fasaha domin yin gogayya da takwarorinsu a duniya.

Ya kuma jaddada buƙatar sa hannun kamfanoni masu zaman kansu wajen bunƙasa ilimi, sannan ya buƙaci tsofaffin ɗaliban jami'o'i da su bayar da tasu gudunmawar ga makarantunsu.

Shettima ya soki yawan yajin aikin da ake fama da shi a ɓangaren ilimi na manyan makarantu, inda ya buƙaci a riƙa tattaunawa da hawa teburin sulhu kan duk wasu matsalolin da suka taso.

Kara karanta wannan

Kashim Shettima ya bayyana hanya 1 da za a magance matsalar tsaro a yankin Arewa maso Gabas

Ya kuma ja kunnen ɗalibai da su guji cin mutuncin jama’a, su jajirce wajen karatunsu domin samun nasarar kammala karatunsu.

Shettima ya kuma ƙaddamar da cibiyar ƙirkire-ƙirkire da kasuwanci ta ƙasa da ƙasa ta Abdulsamad Rabiu wacce aka gina kan kuɗi N1billion a jami'ar Maiduguri.

Tinubu Ya Umarci a Biya Lakcarori Kudinsu

A wani labarin kuma, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya bayar da umarnin a biya malaman jami'o'i albashinsu da aka riƙe.

Hakan ya biyo bayan jingine tsarin "ba aiki, ba biya" da aka kakabawa malaman ASUU kan shafe tsawon watanni takwas suna yajin aiki a 2022.

Asali: Legit.ng

Online view pixel