Aisha Buhari
A labarin nan, za a ji cewa rasuwar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari na ci gaba da yiwa jama'a da dama daci, daga ciki har da diyarsa, Noor.
Ma'aikacin banki kuma malami a jami'ar jihar Yobe, Sheriff Almuhajir ya ce ya yi mafarkin shugaba Muhammadu Buhari ya shiga aljanna bayan birne shi da aka yi.
Mataimakiyar shugaban majalisar dinkin duniya, Amina Mohammed ta yi ta'aziyyar rasuwar shugaba Muhammadu Buhari. Ta ce Buhari ya shiga siyasa don kishin kasa.
An sada tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da makwancinsa na karshe a cikin gidansa da ke Daura. Hakan ya kawo karshen jana'izar marigayin wanda ya rasu.
A yau Talata, 15 ga watan Yuli, 2025 za a yiwa Muhammadu Buhari sutura a birne shi a gidansa da ke Daura a jihar Katsina, ya rasu ne a ƙarshen makon da ya gabata.
Filin jirgin Katsina ya cika da jama'a yayin da aka karbi gawar Muhammadu Buhari daga Landan don binne shi a Daura. Bidiyo ya nuna wadanda suka halarta.
Daruruwan mutane sun yi wa shugaba Muhammadu Buhari sallar gawa daga nesa da ake cewa salatul gha'ib a jihar Gombe. An yi sallar ne a unguwar Pantami.
Gwamnan Katsina, Malam Dikko Umaru Radda da tawagar kwamitin shirya jana'izar tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari sun fara tarbar manyan baƙi.
Shugabannin kasashen duniya da suka hada da Gambiya, Chadi da Guinea Bissau za su halarci jana’izar marigayi Muhammadu Buhari a Daura jihar Katsina.
Aisha Buhari
Samu kari