Aisha Buhari Ta Goyi Bayan Tinubu Kan Sauya Fasalin Takardun Kuɗi

Aisha Buhari Ta Goyi Bayan Tinubu Kan Sauya Fasalin Takardun Kuɗi

  • Aisha Buhari ta nuna inda take goyon baya a tsakanin Tinubu da gwamnan babban bankin Najeriya (CBN)
  • Tinubu ya fitar da wasu matakai waɗanda yake ganin idan CBN yayi aiki da su ba ƙaramin sauƙi ƴan Najeriya za su samu ba
  • Gwamnan CBN na cigaba da haƙiƙancewa takardun tsofaffin kuɗi sun daina aiki a ƙasar nan

Uwar gidan shugaban ƙasa, Aisha Buhari, ta nuna inda take goyon baya a cigaba da tirka-tirkar da ake yi kan shirin sauya fasalin takardun kuɗi na babban bankin Najeriya (CBN) a ƙarƙashin jagorancin Godwin Emefiele.

Uwargidan shugaban ƙasar ta bayyana hakan ne lokacin da ta sanya hoton ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar APC, Bola Tinubu, a shafinta na Instagram sannan ta rubuta: Tinubu ya san hanya.

Aisha Buhari
Aisha Buhari Ta Goyi Bayan Tinubu Kan Sauya Fasalin Takardun Kuɗi
Asali: Depositphotos

Idan za a iya tunawa dai a cikin ƴan kwanakin nan Tinubu ya shawarci CBN kan matakan da yakamata ta ɗauka ɗangane da shirin.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Gwamna Wike Ya Yi Magana Ta Karshe Kan Yuwuwar Sulhu da Atiku Ana Dab da Zaɓen 2023

Aisha Buhari ta nuna ta gamsu da wannan matakai da Tinubu ya shawarci CBN ya ɗauka.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ga matakan kamar haka:

1. Sababbi da tsofaffin kuɗi su cigaba da zama tare a matsayin halastattun kuɗi har zuwa nan da shekara ɗaya.

2. Dakatar da cajin kuɗin da ya shafi tura kuɗi ta yanar gizo da tura kuɗi ta banki da POS har zuwa lokacin da aka kammala warware wannan matsalar.

3. Sanya bankunan kasuwanci da masu hada-hadar kuɗi faɗaɗa wuraren su domin ƙara sauƙaƙawa al'umma.

Sauya fasalin takardun kuɗi na babban bankin Najeriya, ya janyo cece-kuce sosai a ƙasar, a dalilin wahalhalun da ƴan Najeriya suka tsinci kan su a ciki saboda sabon tsarin na sauya fasalin kuɗin.

Emefiele Yaƙar Jam'iyyar APC Yake Yi -Gwamnan APC Ya Fusata

Kara karanta wannan

Karancin Kuɗi: Da Gangan Emefiele Yake Yaƙar APC - Gwamnan APC Ya Ɗau Zafi

A wani labarin na daban kuma, wani babban gwamnan jam'iyyar APC, yayi kakkausar suka kan gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya zargi gwamnan babban bankin da zama wani mai yaƙar jam'iyyar APC akan sauya fasalin tsofaffin takardun kuɗin naira.

Asali: Legit.ng

Online view pixel