‘Yan Sanda Sun Sake Damke Mutane 3, Ana bi Ana Kama Wadanda ke Taba Aisha Buhari

‘Yan Sanda Sun Sake Damke Mutane 3, Ana bi Ana Kama Wadanda ke Taba Aisha Buhari

  • Wasu mutane uku da ake zargin su na da hannu wajen sukar Aisha Muhammadu Buhari sun shiga hannu
  • Ana zargin dakarun ‘yan sandan kasar da yin ram da Salisu Isiyaku, Salisu Habib da wani Zubairu Ahmed
  • Hakan na zuwa ne bayan an kama wani dalibin jami’a bisa zargin cin mutuncin uwargidar shugaban kasar

Abuja - Jami’an ‘yan sandan Najeriya sun kara kaimi wajen yaki da masu sukar uwargidar shugaban kasa, Hajiya Aisha Muhammadu Buhari a Najeriya.

Wani rahoto na musamman da Daily Nigerian ta wallafa, ya bayyana cewa ‘yan sanda sun yi ram da wasu mutane uku, bisa zargin sukar Aisha M. Buhari.

An bada sunayen wadanda aka cafke da Salisu Isiyaku, Salisu Habib da Zubairu Ahmed. Makonni biyu kenan yanzu su na tsare ba a sake jin labarinsu ba.

Kara karanta wannan

Sojan Fadar Shugaban Kasa Ya Bude Wuta, Ya Yi Sanadiyyar Rasa Rai a Abuja

Wata majiya ta ce an kama wadannan mutane uku a ranar 14 ga watan Disamban 2022, aka tsare su a Abuja ba tare da Lauya ko wani 'danuwa ya gana da su ba.

Kaltim Ahmed ta caccaki Aisha Buhari

An cafke wadannan mutane ne a maimakon Kaltim Ahmed, wanda ta fito kwanakin baya ta na sukar matar shugaban kasar saboda kama wani dalibi da aka yi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Maganganun Kaltim sun rika yawo a Whatsapp da sauran dandalin sada zumunta, inda aka ji ta na kalubalantar uwargidar Najeriya ta bada umarni a cafke ta.

Aisha Buhari
Hajiya Aisha Muhammadu Buhari Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

A wani jawabi da tayi a bidiyo, wannan budurwa ta ce kakannin uwargidar shugaban na Najeriya daga ketare suka zo Najeriya bayan sun gama yawo a jeji.

A cewarta, Mai gidanta watau Mai girma Muhammadu Buhari ya yaudari ‘Yan Najeriya sun zabe shi, a karshe ana hallaka mutane amma matarsa tayi shiru.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Sabon Kazamin Hari Hedkwatar 'Yan Sanda, Sun Tashi Bama-Bamai

Salisu Isiyaku ya fada hannu

Shi Salisu Isiyaku da aka cafke, ‘dan canjin kudi ne wanda ya taba saidawa Kaltim Ahmed riyal. Wata majiya a fadar shugaban kasa ce ta fadawa jaridar haka.

Da farko an nemi a zarge shi da hannu wajen harkar ta’addanci amma sai aka gano cewa cinikin da ya kullu tsakaninsu bai kai N500, 000 da za a iya zarginsu ba.

Hakan ta sa ‘yan sanda suka canza zargin da ake yi masa zuwa wani laifin dabam. Kakakin ‘yan sanda, CSP Olumuyiwa Adejobi bai iya magana a kan batun ba.

Idan labarin ya tabbata gaskiya ne, Aisha Buhari wanda ake zargin ta na zaune a Saudi Arabiya tana so wadannan mutane da aka cafke su dandana kudarsu.

Yaro ya ci mutuncin Aisha Buhari

Kwanaki an ji labarin yadda aka tsare Aminu Adam Mohammed na tsawon kwanaki har aka ce zai fuskanci wata kotun Abuja saboda ya zagi Hajiya Aisha Buhari.

Daga baya an janye karar da aka kai dalibin na jami’ar tarayya da ke Dutse a Jigawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel