Abun Bakin Ciki
Kwanaki kadan bayan rasuwar fitaccen jarumin fina-finan Nollywood, John Okafor, an sake rasa wani jigo a masana'antar mai suna Amaechi Muonagor a yau Lahadi.
Ana cikin jimamin rasuwar dalibai mata a jihar Nasarawa, wasu mata huɗu sun sake rasa rayukansu yayin da suka gamu da cunkoso a wurin karbar Zakka a jihar Bauchi.
Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya tura sakon jaje ga iyalan tsohon hadiminsa, Sunday Aghaeze bayan rasuwar matarsa, Mabel Odion Aghaeze a Abuja.
Hukumar Kwastam a yankin jihar Kebbi ta tabbatar da cewa wasu matasa da ake zargin barayin shinkafa ne sun sace buhunnan shinkafa 29 a ofishinsu.
Jarumin fina-finai a Najeriya, Debo Adebayo da aka fi sani da Mr Macaroni ya bayyana yadda ya yi watsi addinin Musulunci da Kiristanci bayan ya yi bincike.
An shiga jimami bayan rasuwar mawaki, Godwin Opara ya na da shekaru 77 a duniya, marigayin da aka fi sani da Kabaka ya rasu ne a yau Juma'a 22 ga watan Maris.
Wasu fusatattun matasa sun lakada wa wani da ake zargin barawon babur dukan tsiya har lahira a garin Magama-Gumau da ke karamar hukumar Toro a jihar Bauchi.
Hukumar EFCC ta sake bankado da maganar karkatar da kudin makamai da ake zargin tsohon shugaban PDP, halliru Bello a mulkin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan.
Mahara sun yi ajalin Dagacin Riruwai da ke karamar hukumar Toro a jihar Bauchi bayan sun yi garkuwa da shi na tsawon kwanaki kafin daga bisani suka hallaka shi.
Abun Bakin Ciki
Samu kari