Abun Al Ajabi
Hukumar kula da abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) ta ce ba ta hana 'yan Najeriya cin burodi da aka buga a kasar ba, sai dai ta ce amfani da saccharin haramun ne.
Rahotanni sun nuna wani mai shayi ya lakaɗawa matashi duka har lahiraa jihar Jigawa kan zarginsa na ɗaukar burodi, madara da indomi, yan sanda sun kama shi.
Basarake a jihar Ondo, Oba Aladetoyinbo Aladelusi ya umarci rufe kasuwanni saboda bikin gargajiya na Aheregbe da aka saba yi a kowace shekara a birnin Akure.
Wani direban Bolt ya bayyana bacin ransa yayin da ya dauko wata mata mai warin jiki a motarsa. Ya ce ba zai iya jure warin da yake dashi ba ko kadan.
Shugaban 'yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun ya ba da labarin yadda Shugaba Bola Tinubu ya sauya rayuwarsa a wata haduwa da suka yi a shekarar 1998.
Rahotanni sun bayyana cewa Maria Branyas, wadda ta fi kowa a duniya ta mutu tana da shekaru 117. An ruwaito cewa an haifi Maria a 1907 kuma ta mutu a Spain.
Abokan huldan bankin GT sun shiga dimuwa bayan wasu da ake zargi 'yan damfara ne sun yi kutse a yanar gizon bankin a yau Laraba da ya jawo matsala.
Gwamnatin jihar Akwa Ibom ta ce 'yan damfara sun yi kutse a lambar WhatsApp din gwamnan jihar, Umo Eno inda har suka fara tura sakon neman kudi daga jama'a.
Fitacciyar jarumar Nollywood, Esther Nwachukwu ta bayyana yadda rayuwarta ta kasance tare da maza daban-daban yayin da ta fadi adadin da ta yi lalata da su.
Abun Al Ajabi
Samu kari