Kano: Bayan Kan-Kan da Kai da Bai Wa Wata Mata Hakuri, Abba Kabir Ya Ja Kunnen Mukarrabansa

Kano: Bayan Kan-Kan da Kai da Bai Wa Wata Mata Hakuri, Abba Kabir Ya Ja Kunnen Mukarrabansa

  • Jim kadan bayan buge motar wata mata da ayarin motocin Gwamna Abba Kabir suka yi, gwamnan ya yi gargadi
  • Abba ya yi gargadi da jan hankalin mukarrabansa da jami'an tsaro kan mutunta mutane a jihar
  • Wannan na zuwa ne bayan gwamnan ya sauko daga motarsa na musamman don bai wa wata mata hakuri

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya gargadi mukarrabansa kan mutunta masoyansu a ko da yaushe.

Abba ya bayyana haka ne yayin da ya ke jan hankalin mukarrabansa da jami'an tsaro bayan buge motar wata mata.

Abba Kabir ya ja hanakalin jami'an tsaro da mukarrabansa kan al'umma
Abba Kabir Ya Gargadi Mukarrabansa kan Mutunta masoyansu. Hoto: Abba Kabir.
Asali: Twitter

Wane jan kunne Abba ya yi?

Gwamnan ya ce duk abin da ya faru babu wanda zai ce jami'an tsaro sai dai ace Abba Gida Gida ne ya wuce ya ci musu mutunci.

Kara karanta wannan

"Ku tuba ko a sheke ku": Wike ya gargadi masu garkuwa da mutane da masu yi masu leken asiri

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma roke su da su gujewa faruwar irin haka a nan gaba ta yadda alummar da suke nuna musu za su ji dadi.

Ya ce:

"Suna tafiya mutane sun yiyo kaina, matasa sun dauka don su na tsaya ni kuma ba dan su na tsaya ba.
"Da kaina na taka don in basu hakuri na ce su sauke gilashi, ana saukewa naga matar gida ce da 'ya'yanta daya a gaba daya a baya.
"Sun shiga firgici da tsoro, na mata magana na ce na sauko ne don in ba ta hakuri abin da aka mata, yaran sun saki jiki sun ji dadi."

Wace shawara Abba ya bayar?

Gwamnan ya kara da cewa:

"Toh irin wadannan abubuwa idan sun faru an wuce ba za a ce jami'an tsaro ba ne suka wuce za a ce Abba Gida Gida ne ya wuce ya mana rashin mutunci

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda Abba Gida-Gida ya sauko daga motarsa don ba wata hakuri, sun bugi motarta ne

"Kun ga kenan madadin ku taimake ni sai ku sani a matsala, ina so mu guji haka saboda nuna wa al'ummar da suke nuna mana kauna muma mu nuna musu kauna."

Wannan na zuwa ne bayan gwamnan ya sauko daga motarsa na musamman don bai wa wata mata hakuri.

Abba Kabir ya dauki matakin saukowa a motarsa ce don bai wa matar hakuri bayan ayarin motocinsa sun buge mata mota.

Abba ya gargadi ciyamomi

Kun ji cewa Gwamnatin jihar Kano a ranar Asabar ta gargadi ciyamomin kananan hukumomi 44 da su daina sayar da kadarorin gwamnati.

Mataimakin gwamnan jihar, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, ya yi gargadin ga ciyamomin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel