Dr. Rilwani Sulaiman Adamu: Buhari ya taya Sarkin Bauchi murnar cika shekaru 50 a duniya

Dr. Rilwani Sulaiman Adamu: Buhari ya taya Sarkin Bauchi murnar cika shekaru 50 a duniya

- Mai martaba Sarkin Bauchi, Rilwanu Suleiman Adamu ya cika shekaru 50 a duniya

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tura sakon gaisuwa da jinjina ga Sarkin a wannan rana

- Buhari ya bayyana wasu kyawawan hallaya na Sarki Adamu da ba za a taba mantawa da su ba

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika sakon taya murna ga sarkin Bauchi, mai martaba Alhaji Rilwanu Suleiman Adamu, a yayinda ya cika shekaru 50 a duniya.

A wani jawabi daga Garba Shehu, babban mai bashi shawara a kafofin watsa labarai, Shugaba Buhari ya yi masa addu’an samun tsawon rai, hikima da karfin jiki yayinda yake ci gaba da jagoranci a kan karagar sarauta.

Shugaban kasar, wanda ya shiga sahun al’umma da gwamnatin jihar Bauchi, musamman majalisar masarautar, wajen taya sarkin mai ran karfe murna, ya yi godiya gare sa a kan yadda yake tafiyar da lamuran jama’a a yankinsa.

KU KARANTA KUMA: Tsohon kakakin majalisar dokokin Jigawa, Illiyasu Dundubus, ya rasu

Dr. Rilwani Sulaiman Adamu: Buhari ya taya Sarkin Bauchi murnar cika shekaru 50 a duniya
Dr. Rilwani Sulaiman Adamu: Buhari ya taya Sarkin Bauchi murnar cika shekaru 50 a duniya Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

Ya kuma yi masa jinjina a kan yadda yake marawa gwamnati baya wajen wayarwa da al’umma kai a kan lamura masu muhimmanci, kamar annobar korona.

Shugaba Buhari ya ce ba za a taba mantawa da jajircewarsa ba ta bangaren sadaqa da tunatar da al’umma muhimmancin juriya, hakuri da kyawawan halayya.

Har ila yau Buhari ya ce sarkin ya cancanci a jinjina masa kan yadda yake kokarin nusar da matasa muhimmancin neman ilimi da rungumar kasuwanci.

KU KARANTA KUMA: FG ta fitar da adireshin yanar gizo na samun tallafin matasa

Daga karshe Shugaban kasaar ya aika sakon gaisuwa ga yan uwa, abokai da hadiman Alhaji Adamu a wannan rana, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

A wani labarin, mun kawo a baya cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya sabon Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli, murnar samun sarautar Zazzau.

Shugaban kasar ya kara da shawartarsa da ya zama shugaba ga kowa da kowa.

Kamar yadda Malam Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasar, ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce wannan lokaci ne mai cike da kalubale.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel