Matakin INEC game da Shugabannin ADC Ya Tafi gaban Trump da Majalisar Amurka
- Kamfanin Amurka ya shirya tattaunawa da Shugaban kasa Donald Trump kan matakin INEC game da shugabancin jam'iyyar ADC
- Hukumar zaben Najeriya ta INEC ta dakatar da amincewa da shugabancin ADC, abin da ya jawo damuwa kan sahihancin zabe mai zuwa
- Kamfanin ya bukaci shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da an yi sahihin zabe da zai nuna ra’ayin ‘yan Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
United States of America – Kamfanin bincike da harkokin siyasa na Amurka, Von Batten-Montague York L.C, ya bayyana shirin tuntuɓar ƴan Majalisar Dokoki da gwamnatin Donald Trump kan batun ADC a Najeriya.
Wannan ya biyo bayan matakin da hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya (INEC) ta ɗauka na dakatar da amincewa da shugabancin jam’iyyar ADC.

Kara karanta wannan
EFCC za ta jika wa Malami aiki, ta jero kadarori kusan 60 da ake so kotu ta kwace

Source: Facebook
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa a cikin wannan mako, INEC ta sanar da cewa ta janye amincewarta ga shugabancin ADC tare da dakatar da duk wata mu’amala ta hukuma da jam’iyyar har sai an kammala shari’ar da ke gudana.
Batun INEC da ADC ya tafi Amurka
Daily Post ta wallafa cewa a cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar jiya, an ce matakin INEC ya dakatar da jam’iyyar adawa mafi girma a Najeriya a wani muhimmin lokaci.
Sanarwar ta kara da cewa wannan muhimmin batu ya jawo damuwa mai kan ingancin dimokuraɗiyya da sahihancin tsarin zabe a kasar musamman gabanin 2027.
Sanarwar ta ce:
“Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya ta janye amincewa ga shugabancin jam’iyyar ADC sannan ta dakatar da duk wata mu’amala da jam’iyyar har sai shari’ar da ke gudana ta kammala."
"Wannan mataki ya dakatar da jam’iyyar adawa mafi girma a Najeriya a wani lokaci mai muhimmanci yayin da take shirin fafatawa a zaben shugaban kasa mai zuwa."
Kamfanin Amurka ta damu da zaɓen Najeriya
Kamfanin Von Batten-Montague York L.C ya ce wannan mataki da hukumar INEC ta dauka zai iya kawo matsala gagarumar gabanin zaben da za a fafata a 2027.
Sanarwar ta ce: “Matakin na iya kawo cikas ga damar jam’iyyar adawa wajen tsara harkokinta da shiga tsarin dimokiradiyya yadda ya kamata."
"A lokacin da ‘yan Najeriya ke sa ran zabe mai ‘yanci, gaskiya, da sahihanci, duk wani lamari da zai iya kawo rudani a harkar siyasa, haifar da rashin tabbas a hukumomi, ko rage 'yancin hukumar zabe, dole ne a magance shi cikin gaggawa da gaskiya.”

Source: Facebook
Haka kuma, kamfanin ya jaddada muhimmancin Najeriya a matsayin babbar dimokuraɗiyya a Afrika da kuma abokin hulɗa mai mahimmanci ga Amurka wajen tsaro, zaman lafiyar tattalin arziki, da yaƙar ta’addanci.
Kamfanin ya ce zai gabatar da damuwarsa ga ƴan Majalisar Dokoki ta Amurka da gwamnatin Trump domin tabbatar da cewa muhimmancin tsarin dimokuradiyya mai gaskiya da ‘yanci a Najeriya yana kan turba.
Haka kuma, an bukaci shugaban kasa Bola Tinubu ya tabbatar da cewa an yi zaben tare da fitar da sakamakon da ƴan nuna ƴan Najeriya za su aminta da shi.
ADC na son Amupitan ya yi murabus
A baya, kun ji cewa jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya ta gudanar da taro bayan hukumar INEC ta janye amincewar da ta yi da shugabanninta.
Shugaban ADC na kasa, Sanata David Mark, ya bayyana cewa ba su da sauran wani kwarin gwiwa kan cewa INEC za ta gudanar da sahihin zabe a 2027.
Hakazalika, Sanata Mark, ya bayyana abin da suke son Shugaban hukumar INEC, Farfesa Joash Amupitan ya yi domin hankalin masu zabe ya kwanta.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

