ADC: Ministan da Tinubu Ya Sauke Ya Fito da Bayanai bayan Batun Ya Sauya Sheka
- Tsohon karamin Ministan raya birane Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo ya yi martani ga bayanan da ke cewa zai rabu da APC
- Yana wannan bayani ne a yayin da jiga-jigan 'yan adawa da ke suke sauya sheka zuwa ADC da ke hamayya da mulkin Bola Tinubu
- Tun bayan Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya sauya sheka zuwa ADC a makon da ya gabata siyasar Kano ta canja alkibla
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Tsohon ƙaramin ministan gidaje da raya birane, Alhaji Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo bai ji dadin rahoton cewa ya sauya sheka ba.
Rahotonni sun rika nuna cewa akwai yiwuwar ya ajiye jam'iyya mai mulki ta APC, tare da sauya sheka zuwa ADC mai tasowa.

Source: Facebook
Sai dai Gwarzo ya yi martani ta cikin wata sanarwa da Mansur Manash Mataimakinsa na musamman kan harkokin yaɗa labarai na zamani ya wallafa a shafin Facebook.
Tsohon ministan Tinubu na tare da APC
Sanarwar ta bayyana cewa tsohon Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo ya tsaya tsayin daka tare da jam’iyyar, har ya bayar da gudunmawa wajen samun ci gaba.
Ta kara da cewa a ‘yan kwanakin nan, an samu jita-jita da rahotanni marasa tushe da ke cewa ATM Gwarzo ya fice daga APC.
Sannan sanarwar da aka fitar ta kara da bayyana cewa duk waɗannan maganganu ƙarya ne da ya kamata jama’a su yi watsi da su.
T. Gwarzo ya jaddada imaninsa da APC
Sanarwar ta kuma jaddada cewa Gwarzo bai taɓa nuna wani yunƙuri ko niyya na barin jam’iyyar ba.
A maimakon haka, yana ci gaba da nuna cikakken goyon baya ga manufofi da hangen nesan APC.

Source: Facebook
Sanarwar ta kuma bayyana cewa Injiniya Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo cikakken ɗan APC ne na gaskiya, kuma ba shi da wata niyya ta barin jam’iyyar a kowane lokaci. Ta kara da cewa duk wani bayani da ke nuna akasin haka an bayyana shi a matsayin yaɗa bayanan ƙarya da nufin rikitar da magoya baya da kuma sauran jama’a. Abdullahi Tijjani Gwarzo ya sake jaddada cewa yana alfahari da kasancewa dan APC, kuma zai ci gaba da aiki tukuru domin ganin jam’iyyar ta samu ci gaba da nasara a gaba.
APC ta san wane ne Rabiu Kwankwaso
A wani labarin, mun wallafa cewa jigon APC, Hon. Farouk Adamu Aliyu, ya ce ba za a iya yin watsi da tasirin jagoran Kwankwasiyya na kasa, Sanata Rabiu Kwankwaso a Kano ba.
Ya bayyana cewa APC na ƙoƙarin fuskantar tasirin Kwankwaso ba tare da raina shi ba yayin da ake shirin zabe mai zuwa domin ta kai da bantenta a zabe mai karatowa.
Hon Farouk Adamu Aliyu ya yi kira ga ‘yan Arewa da ke fushi koo suna ganin an bata masu da su dawo su mara wa jam’iyyar baya domin APC ce hanyar bullewa a kakar zaben 2027.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

