Yadda Sauya Shekar Kwankwaso zuwa ADC Za Ta Iya Shafar Babban Zaben 2027
Kano, Nigeria - Sababbin sauye-sauyen siyasa sun kara daukar hankali a karshen mako yayin da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP a 2023, Sanata Rabiu Kwankwaso ya koma ADC.
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Wannan sauya sheka ta girgiza siyasar Najeriya musamman a Arewa, lamarin da ya sa aka fara hasashen tasirin da Kwankwaso zai iya yi a babban zaben 2027.

Source: Facebook
A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Rabiu Kwankwaso ya tabbatar da ficewarsa daga jam'iyyar NNPP a ranar Lahadi da ta gabata, 29 ga watan Maris, 2026.
Rahotanni sun nuna cewa matakin da Kwankwaso ya dauka ya biyo bayan kammala tattaunawa mai zurfi da shugabannin ADC, a yayin da ake rade-radin yiwuwar hada tikitin takarar shugaban kasa na Obi-Kwankwaso.
A wannan rahoton, Legit Hausa ta yi nazari tare da duba tasirin da wannan sauyi zai iya haifarwa a babban zaben 2027 da ke tafe.
Dalilin Rabiu Kwankwaso na komawa ADC
A watan Afrilun 2025 ne manyan 'yan adawar Najeriya suka amince da ADC a matsayin jama'iyyar da za su ƙulla ƙawance domin tunkarar gwamnatin APC a zaben 2027.
Manyan jagororin wannan hadaka sun kunshi tsohon Mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, dan takarar LP a zaben 2023, Peter Obi da tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai.

Source: Facebook
Tun bayan fara wannan tafiya, aka fara hasashen cewa Kwankwaso na iya shiga ADC, amma daga bisani aka fara danganta shi da APC, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Dangane da dalilin da ya sa Kwankwaso ya zabi ADC maimakon APC, wata majiya ta ce:
“APC ba ta cikin zabinsa tun farko. Wasu sun so ya shiga APC saboda bukatarsu, amma daga baya sun kyale shi.”
Da yake jawabi lokacin da ya yanki katin ADC, Kwankwaso ya ce fitarsa daga NNPP ba abu ne mai sauki ba amma ya zaba dole ya canza jam'iyya domin kawo sauyi a kasa.

Kara karanta wannan
An buga kugen siyasa; Kwankwaso ya sa labule da Atiku, an ji abin da suka tattauna
Ya shaidawa magoya bayansa cewa wannan sauya sheƙar za ta buɗe wani sabon babi na ci gaba da kuma samar da wadata ga daukacin 'yan Najeriya.
Tasirin da Kwankwaso zai iya yi a 2027
Akwai abubuwa da dama suka sa aka fara hasashen cewa komawar madugun Kwankwasiyya ADC zai iya kawo sauyi a babban zaben 2027 da ke kara kusantowa.
1. Tsarin tafiyar Kwankwasiyya
Kwankwaso ba kawai ɗan siyasa daya tilo ba ne, yana wakiltar gagarumin tafiyar siyasa da ke masa biyayya.
Kwankwasiyya, kungiya ce wadda ta yi ƙarfi musamman a Kano da wasu sassan Arewa maso Yamma, kuma ta dade tana nuna ƙarfi, tsari da biyayya.
A zaɓen 2023, duk da ƙarancin yaduwarsa a ƙasa baki ɗaya, ya samu kuri’u masu yawa saboda wannan ginshiƙi, inda ya yi nasarar kafa gwamnati a jihar Kano.
Saboda haka, sauya shekar Kwankwaso zuwa ADC ba sauyin mutum daya kaɗai ba ne, sauyi ne na babbar tawagar magoya baya, wadanda za su iya bada mamaki a 2027.

Source: Facebook
2. Haduwarsa da Atiku da Obi
An dade ana hasashen cewa haduwar manyan kusoshin adawar Najeriya, Atiku Abubakar, Peter Obi da Kwankwaso a inuwar jam'iyya daya, zai iya zama barazana ga gwamnati mai ci.
Duba da sakamakon zaben 2023, wanda Atiku ya zo na biyu, Obi na uku da Kwankwaso na hudu, ana ganin idan suka hadu za su iya samun nasara kan gwamnati mai ci.
Wadannan jagororin adawa sun samu kuri'a kimanin miliyan 1.5 a zaben da ya wuce, hadewarsa za ta iya yin gagarumin tasiri a shekara mai zuwa.
3. Tasirin siyasar Arewa
Yankin Arewacin Najeriya na taka muhimmiyar rawa wajen yanke wanda zai samu nasara a zaɓen shugaban ƙasa saboda yawan masu kada kuri'a
Tasirin Kwankwaso a Kano, ɗaya daga cikin jihohi mafi yawan jama’a, na sa shi zama muhimmin jigo a siyasa.
Idan Kwankwaso ya haɗu da sauran manyan ‘yan siyasa na Arewa kamar Atiku da El-Rufai, ADC na iya zama mai yanke hukunci ko ma ta samu nasara a zabuka masu zuwa.

Source: Facebook
4. Burbudin jam'iyyar NNPP
Alamu sun fara nuna cewa wasu 'ya 'yan jam'iyyar NNPP musamman tsagin Kwankwasiyya za su taya sauran 'yan adawa yakar gwamnatin APC a zaben 2027.
A wata hira da Premier Radio, Hashim Dungurawa ya bayyana cewa za su yi aiki da Rabiu Kwankwaso har sai sun ga bayan Bola Tinubu da Abba Kabir a badi.
Haka zalika Punch ta rahoto Ladipo Johnson yana cewa tsaginsu na NNPP zai hada-kai ne da ADC a zabe.
5. Farin jini wajen talakawa
Rabiu Musa Kwankwaso 'dan siyasa ne mai farin jini sosai wajen talakawa musamman a yankin da ya fito, ana masa ganin wanda zai iya kawo sa'ida idan ya samu dama.
Ana kuka da tsare-tsaren tattalin arzikin Bola Tinubu, har ana ganin sun kara jefa al'umma cikin ni-'ya su, duk da shugaban kasar ya ce yana da kyakkyawar manufa.
'Yan takifen talakawa da yake da su za su iya taimaka wa ADC ta ratsa kauyuka a lokacin da jagororin adawa suke neman yin waje da gwamnatin Bola Tinubu.
Yadda ADC ke shirin tsaida dan takara
A bangaren ADC, jam’iyyar ta ce tana kokarin amfani da tsarin sulhu da masalaha wajen zabar dan takarar shugaban kasa na 2027.
Mai magana da yawun ADC, Bolaji Abdullahi ne ya bayyana hakan a wata hira da gidan talabijin na Arise TV.
Ya ce jam’iyyar na da zabin shirya zaben fitar da gwani ko kuma tsarin masalaha, amma ta fi karkata ga tsarin da kowa zai aminta saboda saukin kashe kudi.
“Muna kokarin samar da amincewar kowa domin shi ne mafi sauki gare mu, kuma wannan ne mafi alheri," in ji shi.
Kwankwaso ya aika sako ga 'yan Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi kira ga daukacin ’yan Najeriya da su dauki zaben 2027 da matukar muhimmanci.
Madugun Kwankwasiyya ya ce lokaci ya yi da yan Najeriya za su cire wasa, su yi abin da ya dace da rayuwarsu a harkokin siyasar kasar nan.
Tsohon dan takarar shugaban kasar ya kuma bukaci magoya bayansa da su tabbata sun mallaki katin zabe (PVC) da kuma katin zama cikakken mamba a jam'iyyar ADC.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng



