Ta Faru Ta Kare: Gawuna Ya Tafi Gidan Kwankwaso Zuwa ADC bayan Barin APC

Ta Faru Ta Kare: Gawuna Ya Tafi Gidan Kwankwaso Zuwa ADC bayan Barin APC

  • Dan takarar gwamnan Kano karkashin jam'iyyar APC a 2023, Nasiru Yusuf Ganuwa ya ziyarci gidan Rabiu Musa Kwankwaso
  • Hakan na zuwa ne bayan ya sanar da ficewar shi daga jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya a shirin haduwa da 'yan adawa a ADC
  • Daya daga cikin jagororin Kwankwasiyyya, Dr Yusuf Kofarmata ya sanar da lokacin da za a karbi Gawuna zuwa ADC a jihar Kano

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Lissafin siyasar Kano ya fara sauyawa bayan jagoran Kwankwasiyyya, Sanata Rabiu Kwankwaso ya fita daga jam'iyyar NNPP zuwa ADC.

Na hannun daman Abdullahi Umar Ganduje kuma tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano, Nasiru Yusuf Gawuna ya fita daga APC.

Nasiru Gawuna da Rabiu Kwankwaso
Lokacin da Nasiru Gawuna ya je gidan Rabiu Kwankwaso. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya wallafa hoton shi da Gawuna a shafinsa na Facebook, alamar da ke nuna sun hada hanyar siyasa a yanzu.

Kara karanta wannan

Bayan shiga ADC, Kwankwaso ya aika sako ga 'yan Najeriya kan zaben 2027

Gawuna ya fita daga jam'iyyar APC

Daily Nigerian ta rahoto tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano kuma fitaccen ɗan siyasa, Nasiru Gawuna, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar APC mai mulki a hukumance.

A cikin wasiƙar murabus da ya rubuta mai ɗauke da kwanan watan 29 ga Maris, 2026, wadda ya aika wa shugaban APC na mazabar Gawuna da ke ƙaramar hukumar Nassarawa a jihar Kano, Gawuna ya ce matakin da ya ɗauka na ficewa daga jam’iyyar:

“Na kashin kansa ne kuma bisa ra’ayinsa.”
“Na sanar da ficewata daga jam’iyyar APC a hukumance, wanda zai fara aiki daga ranar 29 ga Maris, 2026,”

Inji wani ɓangare na wasiƙar.

Gawuna ya tafi gidan Kwankwaso

Biyo bayan fita daga APC, Nasiru Yusuf Gawuna ya garzaya gidan madugun Kwankwasiyyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da ke Miller Road a Kano.

An hango magoya bayan Gawuna sun taka masa baya zuwa Miller Road Kuma an sanya musu jajayen huluna da ke nuna alamar tafiyar Kwankwasiyyya.

Kara karanta wannan

Kwankwaso, Atiku, Obi sun hade kai, sun shirya kayar da Tinubu a zaben 2027

Nasiru Gawuna a gidan Rabiu Kwankwaso
Nasiru Gawuna da mutanen shi a gidan Rabiu Kwankwaso. Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Sai dai a hotunan da aka wallafa a kafafen sadarwa na zamani, ba a ga Nasiru Yusuf Gawuna sanye da jar hula ba, lamarin da ya fara jawo tambayoyi.

Kwankwaso zai karbi Gawuna a ADC

Rahotanni sun bayyana cewa a yau Talata, 31 ga Maris 2026 Sanata Rabiu Kwankwaso zai karbi Nasiru Gawuna zuwa jam'iyyar ADC.

Tsohon Kwamishina a jihar Kano da ya yi murabus daga gwamnatin Abba Kabir Yusuf, Dr Yusuf Ibrahim Kofarmata ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa da misalin karfe 11:00 na safe za a karbi Gawuna.

Kwankwaso ya shiga ADC a hukumance

A wani labarin, mun kawo muku cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya shiga jam'iyyar haɗaka ta ADC a hukumance a wani taro da aka yi a Kano.

Manyan 'yan siyasa da shugabannin ADC a Najeriya da suka hada da shugaban jam'iyyar, David Mark ne suka karbi Kwankwaso a Kano.

A wani taron da aka yi a gidan shi da ke Miller Road, Kwankwaso ya bukaci dukkan 'yan Kwankwasiyyya su yanki katin zama 'yan jam'iyyar ADC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng