Jarumi Sadiq Sani Sadiq Ya Fara Ɗaukar Hankalin Ƴan ADC da Ya Nemi a Canja Tinubu a 2027

Jarumi Sadiq Sani Sadiq Ya Fara Ɗaukar Hankalin Ƴan ADC da Ya Nemi a Canja Tinubu a 2027

  • Kiran fitaccen jarumin Kannywood, Sadiq Sani Sadiq ya faran hankalin ƴan adawa, musamman ƴan jam'iyyar ADC
  • A yan kwanakin nan, Sadiq Sani Sadiq ya fara nuna adawa karara ga salon mulkin Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu gabanin 2027
  • Ya bayyana manyan matsalolin tsaro da suka takura wa mazauna Arewa, musamman jihohin Zamfara, Katsina, da Borno

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Ɗaya daga cikin ƴan ADC, IG Walla ya jinjina wa fitaccen ɗan fim Sadiq Sani Sadiq kan yadda ya fito fili ya yi magana game da matsalar rashin tsaro a Najeriya.

A makon da ake ciki ne wani bidiyo da jarumin ya fitar ya dauki hankulan ƴan Arewa, musamman bayan ya jerin yadda aka bar jihohin Zamfara, Katsina, Borno da Boko Haram da sauran ƴan ta'adda.

Kara karanta wannan

Ana tsakiyar barin wuta, Najeriya za ta amfana da yakin Amurka, Isra'ila da Iran

Yan ADC sun fara nuna goyon baya ga Sadiq Sani Sadiq
Sadiq Sani Sadiq da tambarin ADC a damansa Hoto: @ADCVanguard_/ADC Party
Source: Facebook

Wala ya wallafa a shafin Facebook cewa ana buƙatar irin wannan gwagwarmaya domin kawar da matsalolin da Najeriya ta ke fuskanta.

Jigon ADC ya jinjina wa Sadiq Sani

ADC Vanguard ta wallafa jawabin Wala, inda ya bayyana yunƙurin Sadiq Sani Sadiq a matsayin gwagwarmaya da kishin kasa.

Ya ce:

“Mun gode da yadda ka nuna jajircewa da kishin kasa a lokacin da wasu da yawa ke zaune shiru. Tsayuwarka wajen suka ga yadda ake tafiyar da al'amuran tsaro ya nuna halayenka na gaskiya da damuwa ga al’umma.”

Takardar ta kara da cewa Sadiq ya nuna damuwarsa ga wadanda rikice-rikice suka tilasta wa barin gidajensu da miliyoyin ‘yan Najeriya da ke fama da matsaloli sakamakon manufofin gwamnatin yanzu.

An shawarci Sadiq Sani Sadiq

IG Wala ya bayyana cewa akwai buƙatar a yi wannan tafiya a dunƙule, domin a samu nasarar kawo sauyi da suke ganin Najeriya na bukata.

Kara karanta wannan

Abba Gida Gida ya sauke kwamishinansa a Kano, ya faɗi dalili n yin waje da shi

Wala ya tabbatar wa Sadiq cewa suna tare da shi, inda ya ce:

"Ba kai kadai bane. Kana da goyon bayan al’umma da ke daraja gudummuwarka. Duk wani yunkurin barazana ko cutarwa ga kai saboda amfani da ‘yancin ka na magana zai gamu da martani mai karfi."

Har ila yau, Wala ya ce za a karfafa saƙon Sadiq ga ‘yan Najeriya, tare da jawo hankalin al’umma game da muhimmancin fahimtar halin da ake ciki da shirin makomar kasa.

IG Bwala ya ce ba za su yarda da ƙoƙarin hana Sadiq fadin ra'ayinsa ba
Jarumin Kannywood da ya fara tayar da hazo, Sadiq Sani Sadiq Hoto: IG Wala
Source: Facebook

An kuma bayyana goyon baya ga ra’ayinsa kan rashin daidaito wajen rabon albarkatu da tasirin rashin tsaro a muhimman yankunan noma.

Wala ya shawarci Sadiq ya kirkiri ko samo rubutun fim mai nuna yadda al’umma ke rayuwa cikin matsalolin tsaro da wahala, tare da nuna jarumtakar jama’a.

A zantawarsa da Legit ta waya, Mai Magana da yawun ADC na kasa, Bolaji Abdullahi ya bayyana cewa suna maraba da dukkanin masu son kasa da inganta.

Ya bayyana cewa:

"Aikin ƴan adawa bai ta'allaka da jam'iyyun siyasa kadai ba."

Kara karanta wannan

Ana tsakiyar musayar wuta, Iran ta samu gagarumin goyon baya a yaki da Amurka

Sadiq Sani Sadiq ya waiwayi Tinubu

A baya, mun wallafa cewa fitaccen jarumin Kannywood, Sadiq Sani Sadiq, ya fara fafutukar wayar da kan jama’a game da alaƙar rashin tsaro da shugabanci.

Ya zargi gwamnatin Bola Tinubu da rashin kulawa da yankin Arewa, inda ya jerin jihohin da ke cikin masifar ta'addanci da suka hada da Zamfara, Sakkwato da wadansu jihohi.

Jama’a sun fara bayyana ra’ayoyinsu mabambanta kan wannan kira ganin yawanci ƴan Kannywood na tare da gwamnati, inda ake ganin ya dauko aikin da ya kamata.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng