Lokuta 6 da Sanata Aminu Tambuwal Ya Sauya Sheka a Siyasa

Lokuta 6 da Sanata Aminu Tambuwal Ya Sauya Sheka a Siyasa

Tafiyar siyasar Aminu Waziri Tambuwal, tsohon Kakakin Majalisar Wakilai kuma tsohon gwamnan Sakkwato ta kasance cike da sauya sheƙar jam’iyya sau da dama.

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Sokoto – Tun daga farkon siyasarsa. zuwa abubuwan da ke faruwa a yanzu, Tambuwal na motsa wa daga jam'iyya zuwa jam'iyya, musamman domin neman takara.

Kwanan nan ma, Tambuwal ya yanke shawarar barin PDP domin haɗa kai da ƴan adawa ta ADC domin tunkarar jam’iyya mai mulki gabanin zaɓen 2027.

Tamnuwal ya rika tsalle daga jam'iyya zuwa jam'iyya tun daga shekarar 2007
Tsohon gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal Hoto: Aminu Waziri Tambuwal Media office
Source: Twitter

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa Tambuwal ya ce ya bar jam’iyyar ne sakamakon sabanin da ba za a iya sasanta ba a cikin PDP, inda ya zaɓi komawa siyasa mai inganci a ADC.

Kara karanta wannan

Bukukuwan Sallah: Jerin gwamnonin Arewa 5 da za su biya albashin Maris da wuri

Legit ta tattaro lokutan da Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya sauya sheka a tafiyar siyasarsa kafin ya ci birki yanzu haka a ADC

1. 2007: ANPP zuwa PDP zuwa ANPP

A shekarar 2007, Tambuwal ya fara harkokin siyasarsa a ƙarƙashin jam’iyyar ANPP, ɗaya daga cikin manyan jam’iyyun adawa a lokacin.

Sai dai rikice-rikicen cikin gida kan rabon tikitin takara ya tilasta masa barin jam'iyya..Ya sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP domin samun tikitin takarar majalisa.

Tambuwal ya koma jam'iyyar PDP shekarar 2009
Aminu Tambuwal tare da magoya baya a wani taro a Sakkwato Hoto: Aminu Waziri Tambuwal Media office
Source: Facebook

Daily Trust ta ruwaito daga baya cewa, ‘yan siyasa da dama a wancan lokaci sun koma ƙananan jam’iyyu bayan sun rasa tikiti a manyan jam’iyyu. Daga baya, Tambuwal ya koma jam’iyyar ANPP duk a cikin shekara guda.

2. 2009: ANPP zuwa PDP

Tambuwal ya ɗauki babban mataki a siyasa a shekarar 2009 lokacin da ya shiga jam’iyyar PDP tare da jagoransa na siyasa, Aliyu Wamakko.

A cewar Premium Times a wancan lokaci, sauya shekar wani ɓangare ne na babban sauyin siyasa a Sakkwato, inda Wamakko da magoya bayansa suka fice daga ANPP bayan rikicin cikin gida.

Kara karanta wannan

Ana rade radin tsohon Minista zai rabu da Tinubu, babban makusancinsa ya fice daga APC

Wannan mataki ya zama mai muhimmanci a tafiyar Tambuwal. Da ya tsaya takara a karkashin PDP, ya sake lashe zaɓe zuwa Majalisar Wakilai inda daga bisani ya zama Kakakin Majalisar a shekarar 2011.

3. 2014: PDP zuwa APC

A watan Oktoban 2014, Tambuwal ya sauya sheka daga PDP zuwa APC yayin da yake rike da mukamin Kakakin Majalisar Wakilai a Najeriya.

Tambuwal ya sauya sheka a lokacin yana Majalisar wakilai
Tsohon Shugaban Majalisar wakilai, Aminu Waziri Tambuwal Hoto: Aminu Waziri Tambuwal media office
Source: Twitter

The Cable ta wallafa a wancan lokaci cewa an kuma an ɗauki sauya shekar a matsayin babban rauni ga PDP mai mulki kafin zaɓen 2015.

Yayin sanar da matakinsa, Tambuwal ya ce:

“Bayan na yi shawarwari da mazabata da abokan hulɗata na siyasa, na yanke shawarar shiga jam’iyyar APC.”

Wannan mataki ya haifar da muhawara kan ko ya kamata ya ajiye mukaminsa na Kakaki, amma ya ci gaba da rike mukamin har zuwa ƙarshen wa’adinsa.

Daga bisani ya tsaya takarar gwamna kuma ya lashe zaɓen gwamnan Jihar Sakkwato a shekarar 2015 a karkashin APC.

4. 2018: APC zuwa PDP

A watan Agustan 2018, Tambuwal ya sake sauya sheka zuwa PDP a cewarsa a sakamakon sabani a cikin APC.

Kara karanta wannan

Dan majalisar tarayya a PDP ya hakura, ya bi sahun masu sauya sheka

A cewar rahoton Vanguard, an sanar da sauya shekar tasa ne a wani taro a Sakkwato, inda ya bayyana damuwa kan yadda ake tafiyar da mulki da kuma rikice-rikicen cikin jam’iyya.

Tambuwal ya sake sauya sheƙa zuwa APC
Sanata Aminu Waziri Tambuwal a cikin magoya baya Hoto: Aminu Waziri Tambuwal media office
Source: Facebook

Da ya ke bayyana dalilinsa, Tambuwal ya ce:

“Bayan na yi shawarwari da masu ruwa da tsaki a jihar Sakkwato, na yanke shawarar komawa jam’iyyar PDP.”

Komawarsa PDP ta ba shi damar sake tsayawa takarar gwamna karo na biyu a 2019, wanda ya lashe da ƙyar.

5. 2026: Jam'iyyar PDP zuwa ADC

A watan Maris na 2026, Tambuwal ya sake barin PDP, inda wannan karon ya koma jam’iyyar haɗakar ƴan adawa ga ADC.

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, ya ce murabus ɗinsa yana da alaƙa da rabuwar kai da rikice-rikicen shugabanci a cikin PDP, musamman gabanin zaɓe masu zuwa.

Tambuwal ya koma ADC a shekarar 2026
Sanata Aminu Waziri Tambuwal a lokacin da ya koma ADC Hoto: @AWTambuwal
Source: Twitter

A cikin sanarwar murabus ɗinsa, ya ce:

“Rikice-rikicen cikin gida, sabanin shugabanci da kuma ƙara tsananta rabuwar kai sun sa ba zan iya ci gaba da kasancewa a PDP na.”

Ana kallon komawarsa ADC a matsayin wani ɓangare na sake fasalin siyasar adawa, yayin da ƙananan jam’iyyu ke ƙoƙarin ƙarfafa tasirinsu gabanin zaɓe masu zuwa.

Kara karanta wannan

Bayan ganawa da Tinubu, an ji lokacin da gwamnan Bauchi zai bar PDP zuwa APC

APC ta Harzuƙa Aminu Tambuwal

A baya, mun wallafa cewa Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya zargi shugabancin majalisa da gaggauta amincewa da muhimmin sashe na dokar zaɓen Najeriya.

Aminu Waziri Tambuwal ya yi gargadin cewa hakan na iya buɗe ƙofa ga magudi ganin cewa jam'iyya mai mulki na amfani da karfinta wajen samun yadda ta ke so a majalisa.

Yana wannan batu ne bayan majalisa ta amince da sabuwar dokar zaɓe duk da adawar da sauran jam'iyyu ke yi da sashen aika sakamakon zaɓen gabanin 2027 mai karatowa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng