An ja daga a birnin Shehu yayinda APC ke kokarin tsige Tambuwal

An ja daga a birnin Shehu yayinda APC ke kokarin tsige Tambuwal

-Jam’iyyar APC na kokarin ganin ta tuge Gwamna Tambuwal daga kujerar gwamnan jihar Sokoto

- Dan takarar jam’iyyar, Ahmed Aliyu Sokoto, ya bukaci mutanen jihar da su zabe shi da shugaban kasa Muhammadu Buhari kan rashin ayyukan ci gaba a jihar

- Sanata Aliyu Wamakko, yace dukkanin yan takara na APC a zabe mai zuwa masu martaba ne, inda ya bukaci mutane da su yi waje da jam’iyyar PDP a jihar saboda rashin kokarinta

Rahotanni sun kawo cewa gabannin zaben gwamna na 2019, kullin da ake yi don tsige gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal ya girmama.

A wajen kamfen din dan takarar gwamna na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Dange/Shuni a ranar Lahadin da ya gabata, dan takarar jam’iyyar, Ahmed Aliyu Sokoto, ya bukaci mutanen jihar da su zabe shi da shugaban kasa Muhammadu Buhari kan rashin ayyukan ci gaba a jihar.

An ja daga a birnin Shehu yayinda APC ke kokarin tsige Tambuwal

An ja daga a birnin Shehu yayinda APC ke kokarin tsige Tambuwal
Source: Facebook

A nashi bangaren, shugaban jam’iyyar a jihar, Sanata Aliyu Wamakko, yace dukkanin yan takara na APC a zabe mai zuwa masu martaba ne, inda ya bukaci mutane da su yi waje da jam’iyyar People Democratic Party (PDP) a jihar saboda rashin kokarinta.

KU KARANTA KUMA: Matakin farko da ya kamata gwamnati ta dauka na yaki da cin hanci da rashawa shine tabbatar da yiwa talakawa aiki - Atiku

A wani lamari makamancin haka APC a jihar tace mambobin PDP 10,900 sun sauya sheka zuwa APC a kananan hukumomin Tambuwal da Dange /Shuni da ke jihar.

Hakan na kunshe ne a wani jawabi dauke da sa hannun mataimakinsa a kafofin watsa labarai, Bashir Rabe Mani, a karshen makon da ya gabata.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel