"Kada a Dagula Siyasar Kano": NNPP Ta Aika Sako kan Shirin Tsige Mataimakin Gwamna

"Kada a Dagula Siyasar Kano": NNPP Ta Aika Sako kan Shirin Tsige Mataimakin Gwamna

Jam’iyyar adawa ta NNPP ta bukaci Majalisar Dokokin Kano ta yi taka-tsantsan kan batun tsige mataimakin gwamna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A ranar Alhamis 5 ga watan Maris, 2026 ne Majalisar dokokin Kano ta shaida cewa an fara shirin tsige Aminu AbdulSalam Gwarzo

A cikin jawabin da Kakakin majalisa, Kamaluddeen Sani Shawai ya yi wa Legit, ya bayyana cewa ana zargin Gwarzo da almundahana

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Jam’iyyar NNPP reshen Kano ta yi kira ga Majalisar Dokokin jihar da ta yi taka-tsantsan wajen tafiyar da shirin tsige Mataimakin Gwamna Aminu Abdussalam Gwarzo.

Jam’iyyar ta bayyana cewa duk wani yunkuri na cire zababben jami’in gwamnati daga mukaminsa na bukatar a yi shi cikin hankali da bin doka.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Mataimakin gwamnan Kano na tsaka mai wuya, Majalisa ta tura masa sako

NNPP ta nemi majalisar dokokin Kano ta yi aiki da hankali kan shirin tsige Mataimakin gwamna
Mataimakin gwamnan Kano, Aminu AbdulSalam Gwarzo Hoto: Hon. Balarabe Getso
Source: Facebook

A cikin sanarwar da mai magana da yawun jam'iyya, Injiniya Ibrahim Karaye ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce akwai bukatar a rika sara ana duban bakin gatari musamman a wannan lokaci.

NNPP ta gargadi majalisar Kano

A cikin sanarwar da aka fitar ranar 5 ga Maris, 2026, Ibrahim Karaye ya gargadi ‘yan majalisar da su kauce wa duk wani mataki da zai iya jefa jihar cikin rikicin siyasa.

A cikin sanarwar, jam’iyyar ta jaddada cewa duk wani zababben jami’i yana da ‘yancin bin akidarsa da kuma ra’ayinsa na siyasa ba tare da tilastawa ba.

NNPP ta shawarci gwamnatin Kano game da shirin tsige Gwarzo
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

Ta ce bai dace a matsa wa wani zababben shugaba ya dauki mataki ko ya yanke hukunci da ya saba wa akidarsa ko kuma manufar siyasarsa ba.

Jam’iyyar ta kara da cewa halin da siyasar jihar ke ciki a yanzu yana bukatar shugabanni su nuna hakuri da kuma bin ka’idojin dimokuradiyya.

Kara karanta wannan

Murtala Garo da 'yan siyasa 6 da ake gani za a dauko idan aka tsige Mataimakin gwamnan Kano

Jam'iyyar da ta rasa gwamnanta ga APC a kwanakin baya ta ce ta haka za a kauce wa haifar da sabon rikicin siyasa.

Sakon NNPP ga gwamnatin Kano

Sanarwar ta kuma yi kira ga gwamnatin Kano da ta guji daukar duk wani mataki da zai iya haddasa tashin hankali ko rikici mara amfani, musamman ganin cewa yanayin siyasar jihar a yanzu ya riga ya yi zafi.

NNPP ta kara jaddada cewa 'ya'yanta mutane ne masu bin doka da oda, wadanda ke mutunta dokokin kasa da tsarin dimokuradiyya.

Rahotanni sun nuna cewa wannan gargadin na NNPP ya zo ne bayan ‘yan Majalisar Dokokin Kano sun fara shirin tsige Mataimakin Gwamna Aminu Abdussalam Gwarzo.

Kamar yadda Kakakin majalisar, Kamaluddeen Sani Shawai ya tabbatar wa Legit, ya bayyana cewa an dauki matakin ne bisa wadansu zarge-zarge da ake yi wa Gwarzo.

A kalamansa:

"Mataimakin gwamnan Kano yana da hurumi, yana da dama yana da yanci a kundin tsarin mulki na Najeriya, ya kare kansa."

Ana shirin tsige mataimakin gwamnan Kano

A baya mun wallafa cewa an gabatar da kudirin neman tsige Mataimakin gwamnan Kano, Kwamared Aminu Gwarzo a gaban Majalisar dokoki ranar Alhamis 5 ga watan Maris 2026.

Kara karanta wannan

Ganin Tinubu ya yi biris, MURIC ta canja hanyar neman a tsige Shugaban INEC

Shugaban masu rinjaye a Majalisa, Hon. Lawan Hussaini Dala ne ya gabatar da takardar tuhume-tuhumen da ake yi wa Aminu Gwarzo a zaman da aka yi a ranar.

Shugaban majalisar, Rt. Hon Isma'ila Falgore ya amshi takardar kudirin, kuma ana sa ran za a mika ta ga Mataimakin gwamnan domin ya kare kansa bisa tsarin da doka ta gindaya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng