Tsohon Shugaban Hukumar NIS Ya Shiga APC, Ya Fadi Kujerar da Zai Nema a Jigawa
- Tsohon shugaban hukumar NIS ya ayyana tsayawa takarar sanata a yankin Jigawa ta Arewa maso Gabas a karkashin APC
- Muhammed Babandede zai nemi kujerar sanatan ne bayan ya janye daga takarar gwamna da masoyansa suka so ya nema
- A wata tattaunawa ta wayar tarho, tsohon shugaban hukumar NIS ya fadi dalilin kin neman kujerar gwamna da shirinsa kan 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jigawa - A ranar Lahadi, tsohon shugaban hukumar Immigration (NIS), Muhammed Babandede, ya shiga jam’iyyar APC a hukumance a ƙaramar hukumar Hadejia da ke jihar Jigawa.
Bayan kammala rajistar sa, Babandede ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar sanatan Jigawa ta Arewa maso Gabas a babban zaɓen shekarar 2027.

Source: Twitter
Tsohon shugaban NIS ya shiga APC
Tun lokacin da ya bar ofis a watan Satumban 2021, masana siyasa ke alaƙanta shi da takarar gwamnan jihar Jigawa, zargin da ya kawo karshensa a ranar Talata, in ji rahoton Premium Times.
Da yake magana ta wayar tarho, Babandede ya bayyana cewa magoya bayansa sun matsa masa ya fito takarar gwamna a 2023, amma ya gamsu da salon shugabancin jihar na yanzu.
Muhammed Babandede ya ce:
“Jihar ta yi sa'ar zaɓen Gwamna Umar Namadi a 2023. Duba da ayyukansa, yana da damar ƙarin shekaru huɗu, don haka ba zan nemi takarar gwamna a 2027 ba.”
Ya kuma bayyana cewa rajistar da ya yi a ranar Lahadi abu ne na ƙa'ida kawai, domin ya daɗe yana fafutukar siya a APC, har ma ya yi yakin neman Gwamna Namadi da Shugaba Tinubu a 2023.
A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Babandede ya ce:
"Jiya, na gabatar da katin shaidar rajistar zama dan APC a gundumata ta Kasuwar Kuda da kuma ofishin jam'iyyar na Hadejia, jihar Jigawa.
"Na jaddada biyayya ta ga APC a dukkan matakai. Kuma na jaddada goyon bayana ga Shugaba Bola Tinubu da Gwamna Umar Namadi."
Burin Babandede na neman kujerar sanata
Babandede ya bayyana cewa burinsa na takarar sanata ya samo asali ne daga kiran jama’ar mazabarsa, inda ya yi alƙawarin sauya yadda ake gudanar da wakilci a yankin.

Kara karanta wannan
'Yan daba sun fasa ofishin APC, sun raunata shugaban jam'iyya, tsohon dan majalisa
Ya lura cewa zai mayar da hankali ne kan ayyukan majalisa na ƙwarai, kamar gabatar da dokoki masu amfani da kuma kare haƙƙoƙin jama'ar da yake wakilta.
Muhammed Babandede ya ce:
“Zan kauce wa al’adar raba sukari da sauran kayan abinci a matsayin ayyukan mazaba; maimakon haka, zan mayar da hankali wajen gina cibiyoyi da ilmantar da matasa.”
Ya ƙara da cewa ya riga ya kafa wani kwamiti da zai gudanar da bincike kan ainihin matsalolin da yankin ke fama da su domin gabatar da su ga gwamnatin jiha da ta tarayya.

Source: Facebook
Tarihin rayuwa da aikin Babandede
An haifi Babandede a shekarar 1963 a Jihar Jigawa. Lokacin da yake shugabancin NIS, an san shi wajen kawo sauye-sauyen fasahar zamani a hukumar.
Yana da digiri na farko a fannin Tarihi da Ilimin Musulunci, da kuma digiri na biyu a fannin dokoki da shari’a daga Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zariya.
Tarihin Aiki:
- Ya yi aiki na tsawon shekaru 36 a hukumar shige da fice.
- Ya zama DCG mai kula da sha'anin Fasfo.
- Marigayi Shugaba Muhammadu Buhari ya naɗa shi shugaban NIS a ranar 15 ga Mayu, 2016.
Babandede ya taba kamuwa da COVID-19
A wani rahoto, kun ji cewa, Muhammed Babandede, ya taba kamuwa da cutar COVID-19 a lokacin da annobar ta mamaye duniya a shekarar 2000.
Lokacin da cutar ta kama shi, ya sanar da cewa zai killace kansa na makonni biyu kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya ta umarta.
A lokacin da Babandede, wanda yake shugaban hukumar shige da fice (NIS) yake killace, likitoci sun tabbatar da cewa ya warke daga cutar.
Asali: Legit.ng

