Da dumi-dumi: Hukumar Shige da Fice ta sami sabon shugaba yayin da Babandede ya yi ritaya bayan shekaru 5
- Kwanturola Janar na Hukumar Kula da Shige da Fice ta Najeriya, Muhammad Babandede, ya yi ritaya bayan ya shafe shekaru 36 yana aiki
- Zuwa lokacin da za a nada sabon CG, Idris Isah Jere, Mataimakin Kwanturola Janar ya karbi ragamar aiki
- A yayin bikin barinsa mulki a ranar Juma'a, tsohon CG ya yi alfahari da cewa ya bar NIS fiye da yadda ya same ta
FCT, Abuja - Idris Isah Jere, Mataimakin Kwanturola Janar mai kula da Kudi, ya zama sabon mukaddashin Kwanturola Janar na Hukumar Shige da Fice ta Najeriya (NIS).
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Jere ya karbi mukamin mukaddashin hukumar daga Muhammad Babandede har zuwa lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari zai nada Babban Kwanturola Janar.
Legit.ng ta tattaro cewa Babandede ya yi ritaya bayan ya shafe shekaru 36 yana aiki.
Da yake magana a taron saukarsa daga kujerar shugabanci wanda aka shirya don girmama shi a ranar Juma’a, 10 ga watan Satumba, Babandede ya ce ya bar NIS fiye da yadda ya same ta, jaridar The Cable ta ruwaito.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
CG mai ritaya ya yi alkawarin cewa zai kasance a shirye a koyaushe don taimakawa a duk lokacin da aka kira shi.
Babandede ya kwashe shekaru biyar a matsayin Kwanturola Janar na NIS.
Yan Najeriya sun jinjinawa Babandede
Ameenour Abour Ner'Arlie Kaurah yayi sharhi akan Facebook:
"Bankwana ga sarkin gyara, sarkin ayyuka, CGIS na zamani."
Salisu Muhammad Bello ya ce:
"Wannan babban jami'in tsaro ne mai kwazo da mutunci. Ina yi maka fatan alkairi kwanturolar hukumar kula da shige da fice."
Aliyu Bello ya ce:
"Ya kamata Buhari ya samu wanda zai iya kula da iyakokinmu don gujewa shigowa da makamai masu sauki .... Ina taya ka murna Babandede kan namijin kokarin da kayi!"
Buhari yace yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya yana da matukar wahala
A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis, 9 ga watan Satumba, ya ce yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya ya zama mai matukar wahala.
Shugaban na Najeriya ya bayyana hakan ne a lokacin da yake magana a wani taro tare da shugabannin kudu maso gabas a Owerri yayin ziyarar aiki na kwana daya da ya kai jihar Imo.
Kakakin shugaban kasa, Femi Adesina, ya nakalto shugaban kasar a cikin wata sanarwa a shafin Facebook yana mai cewa babu wanda zai tuhume shi da mallakar kamfanoni ko manyan gidaje a ko ina cikin kasar nan.
Asali: Legit.ng