Shugaban hukumar kula da shige da fice ta Najeriya, Babandede ya warke daga cutar coronavirus

Shugaban hukumar kula da shige da fice ta Najeriya, Babandede ya warke daga cutar coronavirus

Labari da ke zuwa mana ya nuna cewa shugaban hukumar kula da shige da fice ta Najeriya, Muhammad Babandede ya warke daga cutar coronavirus.

Hakan ya biyo bayan gwaji da aka yi masa sau biyu a inda yake killace, inda dukka sakamakon suka nuna baya dauke da cutar kuma.

Kakakin hukumar kula da shige da fice ta kasar, Sunday James, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Talata, 15 ga watan Afrilu a Abuja, jaridar Premium Times ta ruwaito.

Har ila yau Babandede ya gode wa mutanen da suka yi ta yi masa addu'a har ya samu sauki daga cutar ta COVID-19.

Shugaban Immigration, Babandede ya warke daga cutar coronavirus
Shugaban Immigration, Babandede ya warke daga cutar coronavirus
Asali: UGC

Shima da kansa a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Babandede ya ce sakamako na biyu na gwajin da aka yi masa ya nuna cewa ya warke daga cutar.

"Wannan nasara ce daga Allah, muna gode masa da ya ba mu dama muka shiga irin wannan hali wanda ya zarta ilimina da kuma aikin gwamnati," in ji shi.

Babandede na cikin kusoshin gwamnati da suka kamu da coronavirus a Najeriya.

Lokacin da cutar ta kama shi, ya sanar da cewa zai killace kansa na makonni biyu kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya ta umarta.

KU KARANTA KUMA: Annobar Coronavirus: Sakamakon gwajin da aka yi ma wasu mutane 22 a Gombe ya fito

A baya mun ji cewa Babandede ya bayyana cewa kamuwa da yayi da cutar Coronavirus ta sa ya zamto mutum mai tawali’u, tare da kaskantar da kan sa.

Ya bayyana haka ne daga inda aka killace shi a karo na farko, inda yace sakamakon gwajin da aka masa ne ya nuna yana dauke da cutar bayan dawowarsa daga kasar Birtaniya a ranar 22 ga watan Maris.

Babandede ya nemi yan Najeriya su cigaba da addu’ar Allah Ya kiyaye yaduwar cutar, domin kuwa idan hakan ya faru zata kwashi rayukan jama’a da dama.

Kwanturolan ya bayyana haka ne cikin wani bidiyo, inda yace jama’an kauyensu da sauran yan Najeriya suna ta masa addua’r samun sauki.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng