Malaman Addini Sun Hada Kai, Sun Roki Gwamna Ya Ci Gaba da Siyasa bayan 2031

Malaman Addini Sun Hada Kai, Sun Roki Gwamna Ya Ci Gaba da Siyasa bayan 2031

  • Fastocin PFN a jihar Abia sun roƙi Gwamna Alex Otti game da siyasa bayan ya bayyana cewa zai yi ritaya idan ya gama mulkinsa
  • Limaman sun ce kada ya yanke shawara shi kaɗai, su ba jama’a damar tantance makomarsa ta siyasa domin ci gaban jihar
  • Otti ya gode wa coci, ya ce jagorancinsa na karkashin nufin Allah, ba zai yi magana ba sai Ubangiji ya yanke hukunci

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Umuahia, Abia - Fastoci da shugabannin 'Pentecostal Fellowship of Nigeria' reshen jihar Abia sun shawarci gwamnan jihar, Alex Otti.

Fastocin sun bukaci Otti da kada ya janye daga harkokin siyasa bayan kammala wa’adinsa na biyu a shekarar 2031.

An roki gwamna ya yi hakuri ya ci gaba da siyasa
Gwamna Alex Otti na jihar Abia. Hoto: Alex C. Otti.
Source: Facebook

Yadda gwamna ke shirin barin siyasa

Jaridar Punch ta rawaito cewa a watan Disamban 2025, gwamnan ya sake nanata matsayinsa na daina siyasa bayan wa’adinsa, yana mai jaddada cewa hakan shawara ce da ya dade yana rike da ita.

Kara karanta wannan

Aminu Vs Sanusi II: Gwamna Abba ya sake tabo batun rikicin sarautar Kano a gaban Sanata Barau

An ruwaito cewa Otti ya sha bayyana aniyarsa ta janye daga siyasa mai aiki bayan ya kammala wa’adinsa a matsayin gwamna, yana mai cewa ba shi da burin takarar shugaban kasa, mataimakin shugaban kasa ko sanata bayan nan.

Shawarar Faston ga Gwamna Alex Otti

Fastocin sun ba da wannan shawara ne ta bakin tsohon shugaban PFN na jihar, Fasto Chikezie Elekwa, wanda ya jagoranci tawagar zuwa ziyarar girmamawa a ofishin gwamnan.

Elekwa ya ce sun ji labarin shirin gwamnan na barin siyasa bayan wa’adinsa, inda ya roƙe shi da kada ya yanke wannan hukunci shi kaɗai ba tare da jama’a sun yanke ba.

Ya ce:

“Mun ji ka ce bayan wa’adinka na biyu za ka bar siyasa. Don Allah, Mai Girma, kada ka yanke wannan shawara kai kaɗai. Ka bari jama’a su yanke hukunci.”
Fastoci sun ba gwamna shawara game da ci gaba da siyasa
Taswirar jihar Abia da jam'iyyar adawa ta LP ke mulka. Hoto: Legit.
Source: Original

Dalilin Fastocin na hana gwamna ritaya a siyasa

Elekwa ya kara da cewa ba zai dace gwamnan ya bayyana kansa ga jama’a na tsawon shekaru takwas kawai sannan ya ɓace ba, yana mai roƙon a bai wa al’umma damar yanke makomarsa.

Ya kuma tabbatar da cewa gwamnan bai kamata ya damu da kamfen din zaben 2027 ba, domin PFN ta riga ta fara tattara magoya baya a fadin kananan hukumomi da gundumomi.

Kara karanta wannan

An kada hantar Kwankwaso, Barau ya yi alkawari ga Abba, Tinubu kan zaben 2027

A cewarsa:

“Shekara mai zuwa ba ka bukatar kamfen ko’ina. PFN tana tattara mutanenta tun daga tushe, kuma muna tabbatar maka da kuri’unmu.”

Elekwa ya yi alkawarin cikakken goyon bayan coci ga gwamnatin Otti, yana mai cewa Abia ba za ta koma cikin duhu ba, domin hasken da Allah ya kawo ta hannunsa zai kara haskawa.

Da yake mayar da martani, Otti ya gode wa shugabannin PFN bisa addu’o’i, goyon baya da karfafa gwiwa, yana mai amincewa da rawar da coci ta taka a tafiyarsa ta siyasa.

Jam'iyyar LP tana zawarcin Tinubu zuwa cikinta

Mun ba ku labarin cewa mataimakin gwamnan Abia, Ikechukwu Emetu, ya ce jam'iyyarsu a shirye take ta karɓi Shugaba Bola Tinubu daga jam'iyyar APC.

Emetu ya bayyana cewa LP jam’iyya ce mai buɗaɗɗen tsari, wadda ke karɓar kowa ba tare da la’akari da matsayinsa ko jam’iyyarsa ba.

Ya yi watsi da yunƙurin Julius Abure na ƙalubalantar hukuncin kotu, yana cewa LP ta riga ta wuce shi kuma ta koma karkashin sabon jagoranci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.